Al-Zalzalah

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta. إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا
2 Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi. وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا
3 Kuma mutum ya ce "Mẽ neya same ta?" وَقَالَ الْإِنسَانُ مَا لَهَا
4 A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta. يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا
5 cewa Ubangijinka Ya yi umurni zuwa gare ta. بِأَنَّ رَبَّكَ أَوْحَى لَهَا
6 A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu. يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِّيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ
7 To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi. فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ
8 Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi. وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ
;