1 |
Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100001.mp3
|
وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًا |
2 |
Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100002.mp3
|
فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًا |
3 |
Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100003.mp3
|
فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًا |
4 |
Sai su motsar da ƙũra game da shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100004.mp3
|
فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًا |
5 |
Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100005.mp3
|
فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًا |
6 |
Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100006.mp3
|
إِنَّ الْإِنسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ |
7 |
Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa dl haka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100007.mp3
|
وَإِنَّهُ عَلَى ذَلِكَ لَشَهِيدٌ |
8 |
Kuma 1alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100008.mp3
|
وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ |
9 |
Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100009.mp3
|
أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ |
10 |
Aka bayyana abin da ke cikin zukata. |
/content/ayah/audio/hudhaify/100010.mp3
|
وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ |
11 |
Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne? |
/content/ayah/audio/hudhaify/100011.mp3
|
إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌ |