Al-Baiyina

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Waɗanda suka kãfirta daga mũtanen Littafi, da mushirikai, ba su kasance masu gushewa daga gaskiya ba har hujja ta je musu. لَمْ يَكُنِ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ مُنفَكِّينَ حَتَّى تَأْتِيَهُمُ الْبَيِّنَةُ
2 Wani Manzo daga Allah, yana karatun wasu takardu masu tsarki. رَسُولٌ مِّنَ اللَّهِ يَتْلُو صُحُفًا مُّطَهَّرَةً
3 A cikinsu akwai wasu littafai mãsu ƙĩma da daraja. فِيهَا كُتُبٌ قَيِّمَةٌ
4 Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su sãɓa wa juna ba face bayan hujjar ta je musu. وَمَا تَفَرَّقَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ إِلَّا مِن بَعْدِ مَا جَاءتْهُمُ الْبَيِّنَةُ
5 Kuma ba a umarce su da kome ba fãce bauta wa Allah suna mãsu tsarkake addinin gare Shi, mãsu karkata zuwa ga addinin gaskiya, kuma su tsai da salla kuma su bãyar da zakka, kuma wannan shi ne addinin waɗanda suke a kan hanyar ƙwarai. وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ حُنَفَاء وَيُقِيمُوا الصَّلَاةَ وَيُؤْتُوا الزَّكَاةَ وَذَلِكَ دِينُ الْقَيِّمَةِ
6 Lalle ne waɗanda suka kafirta daga mutanen Littafi da mushirikai sana cikin wutar Jahannama suna madawwama a cikinta. Waɗannan su ne mafi ashararancin tãlikai. إِنَّ الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ وَالْمُشْرِكِينَ فِي نَارِ جَهَنَّمَ خَالِدِينَ فِيهَا أُوْلَئِكَ هُمْ شَرُّ الْبَرِيَّةِ
7 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan su ne mafifita alherin halitta. إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُوْلَئِكَ هُمْ خَيْرُ الْبَرِيَّةِ
8 Sakamakonsu, a wurin Ubangijinsu, shi ne gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu sunã madawwama a cikinta har abada. Allah Ya yarda da su, kuma su, sun yarda da Shi. wannan sakamako ne ga wanda ya ji tsõron Ubangijinsa. جَزَاؤُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتُ عَدْنٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا أَبَدًا رَّضِيَ اللَّهُ عَنْهُمْ وَرَضُوا عَنْهُ ذَلِكَ لِمَنْ خَشِيَ رَبَّهُ
;