Al-Alaq

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta. اقْرَأْ بِاسْمِ رَبِّكَ الَّذِي خَلَقَ
2 Ya hahitta mutum daga gudan jini. خَلَقَ الْإِنسَانَ مِنْ عَلَقٍ
3 Ka yi karatu, kuma UbangiJinka shi ne Mafi karimci. اقْرَأْ وَرَبُّكَ الْأَكْرَمُ
4 Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami. الَّذِي عَلَّمَ بِالْقَلَمِ
5 Ya sanar da mutum abin da bai sani ba. عَلَّمَ الْإِنسَانَ مَا لَمْ يَعْلَمْ
6 A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu). كَلَّا إِنَّ الْإِنسَانَ لَيَطْغَى
7 Dõmin yã ga kansa, yã wadãta. أَن رَّآهُ اسْتَغْنَى
8 Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take. إِنَّ إِلَى رَبِّكَ الرُّجْعَى
9 Shin, kã ga wanda ke hana. أَرَأَيْتَ الَّذِي يَنْهَى
10 Bãwã idan yã yi salla? عَبْدًا إِذَا صَلَّى
11 Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya? أَرَأَيْتَ إِن كَانَ عَلَى الْهُدَى
12 Ko ya yi umurni da taƙawa? أَوْ أَمَرَ بِالتَّقْوَى
13 Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya? أَرَأَيْتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّى
14 Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani? أَلَمْ يَعْلَمْ بِأَنَّ اللَّهَ يَرَى
15 A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa. كَلَّا لَئِن لَّمْ يَنتَهِ لَنَسْفَعًا بِالنَّاصِيَةِ
16 Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi. نَاصِيَةٍ كَاذِبَةٍ خَاطِئَةٍ
17 Sai ya kirayi ƙungiyarsa. فَلْيَدْعُ نَادِيَه
18 Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma). سَنَدْعُ الزَّبَانِيَةَ
19 A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u, kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka). كَلَّا لَا تُطِعْهُ وَاسْجُدْ وَاقْتَرِبْ
;