At-Tin

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn. وَالتِّينِ وَالزَّيْتُونِ
2 Da Dũr Sĩnĩna. وَطُورِ سِينِينَ
3 Da wannan gari amintacce. وَهَذَا الْبَلَدِ الْأَمِينِ
4 Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa. لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي أَحْسَنِ تَقْوِيمٍ
5 Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni ثُمَّ رَدَدْنَاهُ أَسْفَلَ سَافِلِينَ
6 Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa. إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ
7 To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)? فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِالدِّينِ
8 Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba? أَلَيْسَ اللَّهُ بِأَحْكَمِ الْحَاكِمِينَ
;