Al-Sharh

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta)? أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ
2 Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe. وَوَضَعْنَا عَنكَ وِزْرَكَ
3 Wanda ya nauyayi bãyanka? الَّذِي أَنقَضَ ظَهْرَكَ
4 Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka? وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ
5 To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا
6 Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi. إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا
7 Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah). فَإِذَا فَرَغْتَ فَانصَبْ
8 Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi. وَإِلَى رَبِّكَ فَارْغَبْ
;