1 |
Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092001.mp3
|
وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَى |
2 |
Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092002.mp3
|
وَالنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّى |
3 |
Da abin da ya halitta namiji da mace. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092003.mp3
|
وَمَا خَلَقَ الذَّكَرَ وَالْأُنثَى |
4 |
Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092004.mp3
|
إِنَّ سَعْيَكُمْ لَشَتَّى |
5 |
To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092005.mp3
|
فَأَمَّا مَن أَعْطَى وَاتَّقَى |
6 |
Kuma ya gaskata kalma mai kyãwo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092006.mp3
|
وَصَدَّقَ بِالْحُسْنَى |
7 |
To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092007.mp3
|
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْيُسْرَى |
8 |
Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092008.mp3
|
وَأَمَّا مَن بَخِلَ وَاسْتَغْنَى |
9 |
Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092009.mp3
|
وَكَذَّبَ بِالْحُسْنَى |
10 |
To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092010.mp3
|
فَسَنُيَسِّرُهُ لِلْعُسْرَى |
11 |
Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta). |
/content/ayah/audio/hudhaify/092011.mp3
|
وَمَا يُغْنِي عَنْهُ مَالُهُ إِذَا تَرَدَّى |
12 |
Lãlle aikinMu ne, Mu bayyana shiriya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092012.mp3
|
إِنَّ عَلَيْنَا لَلْهُدَى |
13 |
Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092013.mp3
|
وَإِنَّ لَنَا لَلْآخِرَةَ وَالْأُولَى |
14 |
Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092014.mp3
|
فَأَنذَرْتُكُمْ نَارًا تَلَظَّى |
15 |
Bãbu mai shigarta sai mafi shaƙãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092015.mp3
|
لَا يَصْلَاهَا إِلَّا الْأَشْقَى |
16 |
Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092016.mp3
|
الَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّى |
17 |
Kuma mafi taƙawa zai nisance ta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092017.mp3
|
وَسَيُجَنَّبُهَا الْأَتْقَى |
18 |
Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092018.mp3
|
الَّذِي يُؤْتِي مَالَهُ يَتَزَكَّى |
19 |
Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092019.mp3
|
وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُ مِن نِّعْمَةٍ تُجْزَى |
20 |
Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/092020.mp3
|
إِلَّا ابْتِغَاء وَجْهِ رَبِّهِ الْأَعْلَى |
21 |
To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi). |
/content/ayah/audio/hudhaify/092021.mp3
|
وَلَسَوْفَ يَرْضَى |