Ash-Shams

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta. وَالشَّمْسِ وَضُحَاهَا
2 Kuma da wata idan ya bi ta. وَالْقَمَرِ إِذَا تَلَاهَا
3 Da yini a lõkacin da ya bayyana ta. وَالنَّهَارِ إِذَا جَلَّاهَا
4 Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta. وَاللَّيْلِ إِذَا يَغْشَاهَا
5 Da sama da abin da ya gina ta. وَالسَّمَاء وَمَا بَنَاهَا
6 Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta. وَالْأَرْضِ وَمَا طَحَاهَا
7 Da rai da abin da ya daidaita shi. وَنَفْسٍ وَمَا سَوَّاهَا
8 Sa'an nan ya sanar da shi fãjircinsa da shiryuwarsa. فَأَلْهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقْوَاهَا
9 Lalle ne wanda ya tsarkake shi (rai) ya sãmi babban rabo. قَدْ أَفْلَحَ مَن زَكَّاهَا
10 Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe shi (da laifi) ya tãɓe. وَقَدْ خَابَ مَن دَسَّاهَا
11 Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu. كَذَّبَتْ ثَمُودُ بِطَغْوَاهَا
12 A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu). إِذِ انبَعَثَ أَشْقَاهَا
13 Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta!" فَقَالَ لَهُمْ رَسُولُ اللَّهِ نَاقَةَ اللَّهِ وَسُقْيَاهَا
14 Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi). فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمْدَمَ عَلَيْهِمْ رَبُّهُم بِذَنبِهِمْ فَسَوَّاهَا
15 Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar). وَلَا يَخَافُ عُقْبَاهَا
;