1 |
Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090001.mp3
|
لَا أُقْسِمُ بِهَذَا الْبَلَدِ |
2 |
Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090002.mp3
|
وَأَنتَ حِلٌّ بِهَذَا الْبَلَدِ |
3 |
Da mahaifi da abin da ya haifa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090003.mp3
|
وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ |
4 |
Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090004.mp3
|
لَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ فِي كَبَدٍ |
5 |
Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/090005.mp3
|
أَيَحْسَبُ أَن لَّن يَقْدِرَ عَلَيْهِ أَحَدٌ |
6 |
Yana cẽwa "Na halakarda dũkiya mai yawa," |
/content/ayah/audio/hudhaify/090006.mp3
|
يَقُولُ أَهْلَكْتُ مَالًا لُّبَدًا |
7 |
Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/090007.mp3
|
أَيَحْسَبُ أَن لَّمْ يَرَهُ أَحَدٌ |
8 |
Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/090008.mp3
|
أَلَمْ نَجْعَل لَّهُ عَيْنَيْنِ |
9 |
Da harshe, da leɓɓa biyu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090009.mp3
|
وَلِسَانًا وَشَفَتَيْنِ |
10 |
Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi biyu ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/090010.mp3
|
وَهَدَيْنَاهُ النَّجْدَيْنِ |
11 |
To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/090011.mp3
|
فَلَا اقْتَحَمَ الْعَقَبَةَ |
12 |
Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã? |
/content/ayah/audio/hudhaify/090012.mp3
|
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْعَقَبَةُ |
13 |
Ita ce fansar wuyan bãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090013.mp3
|
فَكُّ رَقَبَةٍ |
14 |
Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090014.mp3
|
أَوْ إِطْعَامٌ فِي يَوْمٍ ذِي مَسْغَبَةٍ |
15 |
Ga marãya ma'abũcin zumunta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090015.mp3
|
يَتِيمًا ذَا مَقْرَبَةٍ |
16 |
Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090016.mp3
|
أَوْ مِسْكِينًا ذَا مَتْرَبَةٍ |
17 |
Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090017.mp3
|
ثُمَّ كَانَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَتَوَاصَوْا بِالصَّبْرِ وَتَوَاصَوْا بِالْمَرْحَمَةِ |
18 |
Waɗannan ne ma'abũta albarka |
/content/ayah/audio/hudhaify/090018.mp3
|
أُوْلَئِكَ أَصْحَابُ الْمَيْمَنَةِ |
19 |
Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyinMu, sũ ne ma'abũta shu'umci |
/content/ayah/audio/hudhaify/090019.mp3
|
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِنَا هُمْ أَصْحَابُ الْمَشْأَمَةِ |
20 |
A kansu akwai wata wuta abar kullewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/090020.mp3
|
عَلَيْهِمْ نَارٌ مُّؤْصَدَةٌ |