1 |
Inã rantsuwa da alfijiri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089001.mp3
|
وَالْفَجْرِ |
2 |
Da darũruwa gõma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089002.mp3
|
وَلَيَالٍ عَشْرٍ |
3 |
Da (adadi na) cikã da (na) mãrã. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089003.mp3
|
وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ |
4 |
Da dare idan yana shũɗewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089004.mp3
|
وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ |
5 |
Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/089005.mp3
|
هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَمٌ لِّذِي حِجْرٍ |
6 |
Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/089006.mp3
|
أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ |
7 |
Iramawa mãsu sakon ƙĩrar jiki. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089007.mp3
|
إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ |
8 |
Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya). |
/content/ayah/audio/hudhaify/089008.mp3
|
الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلَادِ |
9 |
Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi suka yi gidãje)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/089009.mp3
|
وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ |
10 |
Da Fir'auna mai turãku. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089010.mp3
|
وَفِرْعَوْنَ ذِي الْأَوْتَادِ |
11 |
Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/089011.mp3
|
الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلَادِ |
12 |
Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089012.mp3
|
فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ |
13 |
Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089013.mp3
|
فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ |
14 |
Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089014.mp3
|
إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ |
15 |
To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni." |
/content/ayah/audio/hudhaify/089015.mp3
|
فَأَمَّا الْإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ |
16 |
Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni." |
/content/ayah/audio/hudhaify/089016.mp3
|
وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ |
17 |
A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya! |
/content/ayah/audio/hudhaify/089017.mp3
|
كَلَّا بَل لَّا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ |
18 |
Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci! |
/content/ayah/audio/hudhaify/089018.mp3
|
وَلَا تَحَاضُّونَ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ |
19 |
Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089019.mp3
|
وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا |
20 |
Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089020.mp3
|
وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا |
21 |
A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089021.mp3
|
كَلَّا إِذَا دُكَّتِ الْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا |
22 |
Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, safũ- safu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089022.mp3
|
وَجَاء رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا |
23 |
Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi! |
/content/ayah/audio/hudhaify/089023.mp3
|
وَجِيءَ يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ وَأَنَّى لَهُ الذِّكْرَى |
24 |
Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/089024.mp3
|
يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي |
25 |
To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089025.mp3
|
فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُ أَحَدٌ |
26 |
Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurinSa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/089026.mp3
|
وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُ أَحَدٌ |
27 |
Yã kai rai mai natsuwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/089027.mp3
|
يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ |
28 |
Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira). |
/content/ayah/audio/hudhaify/089028.mp3
|
ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً |
29 |
Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyiNa (mãsu bin umurui a dũniya). |
/content/ayah/audio/hudhaify/089029.mp3
|
فَادْخُلِي فِي عِبَادِي |
30 |
Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira). |
/content/ayah/audio/hudhaify/089030.mp3
|
وَادْخُلِي جَنَّتِي |