1 |
Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka? |
/content/ayah/audio/hudhaify/088001.mp3
|
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْغَاشِيَةِ |
2 |
Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088002.mp3
|
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ خَاشِعَةٌ |
3 |
Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088003.mp3
|
عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ |
4 |
Zã su shiga wata wuta mai zãfi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088004.mp3
|
تَصْلَى نَارًا حَامِيَةً |
5 |
Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088005.mp3
|
تُسْقَى مِنْ عَيْنٍ آنِيَةٍ |
6 |
Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088006.mp3
|
لَّيْسَ لَهُمْ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ |
7 |
Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088007.mp3
|
لَا يُسْمِنُ وَلَا يُغْنِي مِن جُوعٍ |
8 |
Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088008.mp3
|
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ |
9 |
Game da aikinsu, masu yarda ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088009.mp3
|
لِسَعْيِهَا رَاضِيَةٌ |
10 |
(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088010.mp3
|
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ |
11 |
Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088011.mp3
|
لَّا تَسْمَعُ فِيهَا لَاغِيَةً |
12 |
A cikinta akwai marmaro mai gudãna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088012.mp3
|
فِيهَا عَيْنٌ جَارِيَةٌ |
13 |
A cikinta akwai gadãje maɗaukaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088013.mp3
|
فِيهَا سُرُرٌ مَّرْفُوعَةٌ |
14 |
Da kõfuna ar'aje. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088014.mp3
|
وَأَكْوَابٌ مَّوْضُوعَةٌ |
15 |
Da filõli jẽre, |
/content/ayah/audio/hudhaify/088015.mp3
|
وَنَمَارِقُ مَصْفُوفَةٌ |
16 |
Da katifu shimfiɗe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088016.mp3
|
وَزَرَابِيُّ مَبْثُوثَةٌ |
17 |
Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su? |
/content/ayah/audio/hudhaify/088017.mp3
|
أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ |
18 |
Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta? |
/content/ayah/audio/hudhaify/088018.mp3
|
وَإِلَى السَّمَاء كَيْفَ رُفِعَتْ |
19 |
Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su? |
/content/ayah/audio/hudhaify/088019.mp3
|
وَإِلَى الْجِبَالِ كَيْفَ نُصِبَتْ |
20 |
Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta? |
/content/ayah/audio/hudhaify/088020.mp3
|
وَإِلَى الْأَرْضِ كَيْفَ سُطِحَتْ |
21 |
sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088021.mp3
|
فَذَكِّرْ إِنَّمَا أَنتَ مُذَكِّرٌ |
22 |
Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088022.mp3
|
لَّسْتَ عَلَيْهِم بِمُصَيْطِرٍ |
23 |
Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088023.mp3
|
إِلَّا مَن تَوَلَّى وَكَفَرَ |
24 |
To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088024.mp3
|
فَيُعَذِّبُهُ اللَّهُ الْعَذَابَ الْأَكْبَرَ |
25 |
Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088025.mp3
|
إِنَّ إِلَيْنَا إِيَابَهُمْ |
26 |
Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/088026.mp3
|
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا حِسَابَهُمْ |