At-Tariq

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare. وَالسَّمَاء وَالطَّارِقِ
2 To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare? وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ
3 Shi ne taurãron nan mai tsananin haske. النَّجْمُ الثَّاقِبُ
4 Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro. إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ
5 To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi? فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ مِمَّ خُلِقَ
6 An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna. خُلِقَ مِن مَّاء دَافِقٍ
7 Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji. يَخْرُجُ مِن بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ
8 Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne. إِنَّهُ عَلَى رَجْعِهِ لَقَادِرٌ
9 Rãnar da ake jarrabawar asirai. يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ
10 Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah). فَمَا لَهُ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ
11 Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa. وَالسَّمَاء ذَاتِ الرَّجْعِ
12 Da ƙasa ma'abũciyar tsãgẽwa, وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ
13 Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ
14 Kuma shĩ bã bananci bane وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ
15 Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai. إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا
16 Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi. وَأَكِيدُ كَيْدًا
17 Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu. فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا
;