An-Nabaa

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 A kan mẽ suke tambayar jũna? عَمَّ يَتَسَاءلُونَ
2 A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni)? عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ
3 Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa? الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ
4 A'aha! Zã su sani. كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
5 Kuma, a'aha! Zã su sani. ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ
6 Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba? أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا
7 Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa)? وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا
8 Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã? وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا
9 Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa? وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا
10 Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura? وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا
11 Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci? وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا
12 Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi? وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا
13 Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã)? وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا
14 Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba? وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاء ثَجَّاجًا
15 Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi? لِنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا
16 Da itãcen lambuna mãsu lillibniya? وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا
17 Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci. إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا
18 Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a. يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا
19 Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi. وَفُتِحَتِ السَّمَاء فَكَانَتْ أَبْوَابًا
20 Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra. وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا
21 Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata. إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا
22 Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma. لِلْطَّاغِينَ مَآبًا
23 Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna. لَابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا
24 Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha. لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا
25 Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini. إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا
26 Sakamako mai dãcẽwa. جَزَاء وِفَاقًا
27 Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi. إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا
28 Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa! وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا
29 Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce. وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا
30 Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba. فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا
31 Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo. إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا
32 Lambuna da inabõbi. حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا
33 Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna. وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا
34 Da hinjãlan giya cikakku. وَكَأْسًا دِهَاقًا
35 Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa. لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا
36 Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa. جَزَاء مِّن رَّبِّكَ عَطَاء حِسَابًا
37 Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi. رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرحْمَنِ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا
38 Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai. يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرحْمَنُ وَقَالَ صَوَابًا
39 Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa. ذَلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ فَمَن شَاء اتَّخَذَ إِلَى رَبِّهِ مَآبًا
40 Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya!" إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا
;