An-Nazi'at

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi. وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا
2 Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi. وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا
3 Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo. وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا
4 Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umurnin Allah) kamar suna tsẽre. فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا
5 Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni. فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا
6 Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa. يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ
7 Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye. تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ
8 Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne. قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ
9 Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu. أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ
10 Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? يَقُولُونَ أَئِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ
11 "Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu?" أَئِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً
12 Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya!" قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ
13 To, ita kam, tsãwa guda kawai ce. فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ
14 Sai kawai gã su a bãyan ƙasa. فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ
15 Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka? هَلْ أتَاكَ حَدِيثُ مُوسَى
16 A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã? إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى
17 Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi. اذْهَبْ إِلَى فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَى
18 "Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَى أَن تَزَكَّى
19 "Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa?" وَأَهْدِيَكَ إِلَى رَبِّكَ فَتَخْشَى
20 Sai ya nũna masa ãyar nan mafi girma. فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَى
21 Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni), فَكَذَّبَ وَعَصَى
22 Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri. ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَى
23 Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira. فَحَشَرَ فَنَادَى
24 Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka." فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَى
25 Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko. فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَى
26 Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah. إِنَّ فِي ذَلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَى
27 Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta. أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاء بَنَاهَا
28 Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta. رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا
29 Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta. وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا
30 Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta. وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَلِكَ دَحَاهَا
31 Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta. أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءهَا وَمَرْعَاهَا
32 Da duwatsu, Yã kafe ta. وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا
33 Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku. مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ
34 To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo. فَإِذَا جَاءتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَى
35 Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata. يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَى
36 Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani. وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَى
37 To, amma wanda ya yi girman kai. فَأَمَّا مَن طَغَى
38 Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya). وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا
39 To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma. فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَى
40 Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai. وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَى
41 To, lalle ne Aljanna ita ce makõma. فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَى
42 Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta? يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا
43 Me ya haɗã ka da ambatonta? فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا
44 Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake. إِلَى رَبِّكَ مُنتَهَاهَا
45 Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta. إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا
46 Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa. كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا
;