1 |
Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077001.mp3
|
وَالْمُرْسَلَاتِ عُرْفًا |
2 |
Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077002.mp3
|
فَالْعَاصِفَاتِ عَصْفًا |
3 |
Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077003.mp3
|
وَالنَّاشِرَاتِ نَشْرًا |
4 |
sa'an nan, da ãyõyi mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077004.mp3
|
فَالْفَارِقَاتِ فَرْقًا |
5 |
Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077005.mp3
|
فَالْمُلْقِيَاتِ ذِكْرًا |
6 |
Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077006.mp3
|
عُذْرًا أَوْ نُذْرًا |
7 |
Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne |
/content/ayah/audio/hudhaify/077007.mp3
|
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَاقِعٌ |
8 |
To, idan taurãri aka shãfe haskensu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077008.mp3
|
فَإِذَا النُّجُومُ طُمِسَتْ |
9 |
Kuma, idan sama aka tsãge ta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077009.mp3
|
وَإِذَا السَّمَاء فُرِجَتْ |
10 |
Kuma, idan duwãtsu aka nike su. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077010.mp3
|
وَإِذَا الْجِبَالُ نُسِفَتْ |
11 |
Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077011.mp3
|
وَإِذَا الرُّسُلُ أُقِّتَتْ |
12 |
Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077012.mp3
|
لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ |
13 |
Domin rãnar rarrabẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077013.mp3
|
لِيَوْمِ الْفَصْلِ |
14 |
Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/077014.mp3
|
وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الْفَصْلِ |
15 |
Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077015.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
16 |
Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077016.mp3
|
أَلَمْ نُهْلِكِ الْأَوَّلِينَ |
17 |
Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe? |
/content/ayah/audio/hudhaify/077017.mp3
|
ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ الْآخِرِينَ |
18 |
Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077018.mp3
|
كَذَلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ |
19 |
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077019.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
20 |
Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077020.mp3
|
أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّاء مَّهِينٍ |
21 |
Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077021.mp3
|
فَجَعَلْنَاهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ |
22 |
Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077022.mp3
|
إِلَى قَدَرٍ مَّعْلُومٍ |
23 |
Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077023.mp3
|
فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ الْقَادِرُونَ |
24 |
Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077024.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
25 |
Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077025.mp3
|
أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ كِفَاتًا |
26 |
Ga rãyayyu da matattu, |
/content/ayah/audio/hudhaify/077026.mp3
|
أَحْيَاء وَأَمْوَاتًا |
27 |
Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi? |
/content/ayah/audio/hudhaify/077027.mp3
|
وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ شَامِخَاتٍ وَأَسْقَيْنَاكُم مَّاء فُرَاتًا |
28 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077028.mp3
|
وَيْلٌ يوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
29 |
Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077029.mp3
|
انطَلِقُوا إِلَى مَا كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ |
30 |
Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077030.mp3
|
انطَلِقُوا إِلَى ظِلٍّ ذِي ثَلَاثِ شُعَبٍ |
31 |
Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077031.mp3
|
لَا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِي مِنَ اللَّهَبِ |
32 |
Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077032.mp3
|
إِنَّهَا تَرْمِي بِشَرَرٍ كَالْقَصْرِ |
33 |
Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077033.mp3
|
كَأَنَّهُ جِمَالَتٌ صُفْرٌ |
34 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077034.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
35 |
Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077035.mp3
|
هَذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ |
36 |
Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077036.mp3
|
وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ |
37 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077037.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
38 |
Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077038.mp3
|
هَذَا يَوْمُ الْفَصْلِ جَمَعْنَاكُمْ وَالْأَوَّلِينَ |
39 |
To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077039.mp3
|
فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ |
40 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077040.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
41 |
Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077041.mp3
|
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي ظِلَالٍ وَعُيُونٍ |
42 |
Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077042.mp3
|
وَفَوَاكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ |
43 |
(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa." |
/content/ayah/audio/hudhaify/077043.mp3
|
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ |
44 |
Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/077044.mp3
|
إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنينَ |
45 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077045.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
46 |
(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/077046.mp3
|
كُلُوا وَتَمَتَّعُوا قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ |
47 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077047.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
48 |
Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba." |
/content/ayah/audio/hudhaify/077048.mp3
|
وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ارْكَعُوا لَا يَرْكَعُونَ |
49 |
Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/077049.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
50 |
To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni |
/content/ayah/audio/hudhaify/077050.mp3
|
فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ |