1 |
Kiran gaskiya! |
/content/ayah/audio/hudhaify/069001.mp3
|
الْحَاقَّةُ |
2 |
Mẽne ne kiran gaskiya? |
/content/ayah/audio/hudhaify/069002.mp3
|
مَا الْحَاقَّةُ |
3 |
Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya? |
/content/ayah/audio/hudhaify/069003.mp3
|
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحَاقَّةُ |
4 |
Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya! |
/content/ayah/audio/hudhaify/069004.mp3
|
كَذَّبَتْ ثَمُودُ وَعَادٌ بِالْقَارِعَةِ |
5 |
To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069005.mp3
|
فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهْلِكُوا بِالطَّاغِيَةِ |
6 |
Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069006.mp3
|
وَأَمَّا عَادٌ فَأُهْلِكُوا بِرِيحٍ صَرْصَرٍ عَاتِيَةٍ |
7 |
(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069007.mp3
|
سَخَّرَهَا عَلَيْهِمْ سَبْعَ لَيَالٍ وَثَمَانِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًا فَتَرَى الْقَوْمَ فِيهَا صَرْعَى كَأَنَّهُمْ أَعْجَازُ نَخْلٍ خَاوِيَةٍ |
8 |
To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu? |
/content/ayah/audio/hudhaify/069008.mp3
|
فَهَلْ تَرَى لَهُم مِّن بَاقِيَةٍ |
9 |
Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069009.mp3
|
وَجَاء فِرْعَوْنُ وَمَن قَبْلَهُ وَالْمُؤْتَفِكَاتُ بِالْخَاطِئَةِ |
10 |
Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani). |
/content/ayah/audio/hudhaify/069010.mp3
|
فَعَصَوْا رَسُولَ رَبِّهِمْ فَأَخَذَهُمْ أَخْذَةً رَّابِيَةً |
11 |
Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069011.mp3
|
إِنَّا لَمَّا طَغَى الْمَاء حَمَلْنَاكُمْ فِي الْجَارِيَةِ |
12 |
Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi). |
/content/ayah/audio/hudhaify/069012.mp3
|
لِنَجْعَلَهَا لَكُمْ تَذْكِرَةً وَتَعِيَهَا أُذُنٌ وَاعِيَةٌ |
13 |
To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069013.mp3
|
فَإِذَا نُفِخَ فِي الصُّورِ نَفْخَةٌ وَاحِدَةٌ |
14 |
Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069014.mp3
|
وَحُمِلَتِ الْأَرْضُ وَالْجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَاحِدَةً |
15 |
A ran nan, mai aukuwa zã ta auku. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069015.mp3
|
فَيَوْمَئِذٍ وَقَعَتِ الْوَاقِعَةُ |
16 |
Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069016.mp3
|
وَانشَقَّتِ السَّمَاء فَهِيَ يَوْمَئِذٍ وَاهِيَةٌ |
17 |
Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069017.mp3
|
وَالْمَلَكُ عَلَى أَرْجَائِهَا وَيَحْمِلُ عَرْشَ رَبِّكَ فَوْقَهُمْ يَوْمَئِذٍ ثَمَانِيَةٌ |
18 |
A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069018.mp3
|
يَوْمَئِذٍ تُعْرَضُونَ لَا تَخْفَى مِنكُمْ خَافِيَةٌ |
19 |
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069019.mp3
|
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ فَيَقُولُ هَاؤُمُ اقْرَؤُوا كِتَابِيهْ |
20 |
"Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069020.mp3
|
إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَاقٍ حِسَابِيهْ |
21 |
Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069021.mp3
|
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ |
22 |
A cikin Aljanna maɗaukakiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069022.mp3
|
فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ |
23 |
Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba), |
/content/ayah/audio/hudhaify/069023.mp3
|
قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ |
24 |
(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069024.mp3
|
كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا أَسْلَفْتُمْ فِي الْأَيَّامِ الْخَالِيَةِ |
25 |
Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/069025.mp3
|
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِشِمَالِهِ فَيَقُولُ يَا لَيْتَنِي لَمْ أُوتَ كِتَابِيهْ |
26 |
"Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/069026.mp3
|
وَلَمْ أَدْرِ مَا حِسَابِيهْ |
27 |
"In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce! |
/content/ayah/audio/hudhaify/069027.mp3
|
يَا لَيْتَهَا كَانَتِ الْقَاضِيَةَ |
28 |
"Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/069028.mp3
|
مَا أَغْنَى عَنِّي مَالِيهْ |
29 |
"Ĩkona ya ɓace mini!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/069029.mp3
|
هَلَكَ عَنِّي سُلْطَانِيهْ |
30 |
(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069030.mp3
|
خُذُوهُ فَغُلُّوهُ |
31 |
"Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069031.mp3
|
ثُمَّ الْجَحِيمَ صَلُّوهُ |
32 |
"Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069032.mp3
|
ثُمَّ فِي سِلْسِلَةٍ ذَرْعُهَا سَبْعُونَ ذِرَاعًا فَاسْلُكُوهُ |
33 |
"Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/069033.mp3
|
إِنَّهُ كَانَ لَا يُؤْمِنُ بِاللَّهِ الْعَظِيمِ |
34 |
"Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/069034.mp3
|
وَلَا يَحُضُّ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ |
35 |
"Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069035.mp3
|
فَلَيْسَ لَهُ الْيَوْمَ هَاهُنَا حَمِيمٌ |
36 |
"Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069036.mp3
|
وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنْ غِسْلِينٍ |
37 |
"Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci." |
/content/ayah/audio/hudhaify/069037.mp3
|
لَا يَأْكُلُهُ إِلَّا الْخَاطِؤُونَ |
38 |
To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba, |
/content/ayah/audio/hudhaify/069038.mp3
|
فَلَا أُقْسِمُ بِمَا تُبْصِرُونَ |
39 |
Da abin da bã ku iya gani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069039.mp3
|
وَمَا لَا تُبْصِرُونَ |
40 |
Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069040.mp3
|
إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ |
41 |
Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069041.mp3
|
وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَاعِرٍ قَلِيلًا مَا تُؤْمِنُونَ |
42 |
Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069042.mp3
|
وَلَا بِقَوْلِ كَاهِنٍ قَلِيلًا مَا تَذَكَّرُونَ |
43 |
Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069043.mp3
|
تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ الْعَالَمِينَ |
44 |
Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069044.mp3
|
وَلَوْ تَقَوَّلَ عَلَيْنَا بَعْضَ الْأَقَاوِيلِ |
45 |
Dã Mun kãma shi da dãma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069045.mp3
|
لَأَخَذْنَا مِنْهُ بِالْيَمِينِ |
46 |
sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069046.mp3
|
ثُمَّ لَقَطَعْنَا مِنْهُ الْوَتِينَ |
47 |
Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbarMu) daga gare shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069047.mp3
|
فَمَا مِنكُم مِّنْ أَحَدٍ عَنْهُ حَاجِزِينَ |
48 |
Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069048.mp3
|
وَإِنَّهُ لَتَذْكِرَةٌ لِّلْمُتَّقِينَ |
49 |
Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069049.mp3
|
وَإِنَّا لَنَعْلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ |
50 |
Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069050.mp3
|
وَإِنَّهُ لَحَسْرَةٌ عَلَى الْكَافِرِينَ |
51 |
Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙshẽni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069051.mp3
|
وَإِنَّهُ لَحَقُّ الْيَقِينِ |
52 |
Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/069052.mp3
|
فَسَبِّحْ بِاسْمِ رَبِّكَ الْعَظِيمِ |