1 |
Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070001.mp3
|
سَأَلَ سَائِلٌ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ |
2 |
Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070002.mp3
|
لِّلْكَافِرينَ لَيْسَ لَهُ دَافِعٌ |
3 |
Daga Allah Mai matãkala. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070003.mp3
|
مِّنَ اللَّهِ ذِي الْمَعَارِجِ |
4 |
Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070004.mp3
|
تَعْرُجُ الْمَلَائِكَةُ وَالرُّوحُ إِلَيْهِ فِي يَوْمٍ كَانَ مِقْدَارُهُ خَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ |
5 |
Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070005.mp3
|
فَاصْبِرْ صَبْرًا جَمِيلًا |
6 |
Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070006.mp3
|
إِنَّهُمْ يَرَوْنَهُ بَعِيدًا |
7 |
Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070007.mp3
|
وَنَرَاهُ قَرِيبًا |
8 |
Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070008.mp3
|
يَوْمَ تَكُونُ السَّمَاء كَالْمُهْلِ |
9 |
Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070009.mp3
|
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ |
10 |
Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070010.mp3
|
وَلَا يَسْأَلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا |
11 |
Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/070011.mp3
|
يُبَصَّرُونَهُمْ يَوَدُّ الْمُجْرِمُ لَوْ يَفْتَدِي مِنْ عَذَابِ يَوْمِئِذٍ بِبَنِيهِ |
12 |
Da matarsa da ɗan'uwansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070012.mp3
|
وَصَاحِبَتِهِ وَأَخِيهِ |
13 |
Da danginsa, mãsu tattarã shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070013.mp3
|
وَفَصِيلَتِهِ الَّتِي تُؤْويهِ |
14 |
Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070014.mp3
|
وَمَن فِي الْأَرْضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ |
15 |
A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã, |
/content/ayah/audio/hudhaify/070015.mp3
|
كَلَّا إِنَّهَا لَظَى |
16 |
Mai twãle fãtar goshi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070016.mp3
|
نَزَّاعَةً لِّلشَّوَى |
17 |
Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070017.mp3
|
تَدْعُو مَنْ أَدْبَرَ وَتَوَلَّى |
18 |
Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070018.mp3
|
وَجَمَعَ فَأَوْعَى |
19 |
Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070019.mp3
|
إِنَّ الْإِنسَانَ خُلِقَ هَلُوعًا |
20 |
Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070020.mp3
|
إِذَا مَسَّهُ الشَّرُّ جَزُوعًا |
21 |
Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070021.mp3
|
وَإِذَا مَسَّهُ الْخَيْرُ مَنُوعًا |
22 |
Sai mãsu yin salla, |
/content/ayah/audio/hudhaify/070022.mp3
|
إِلَّا الْمُصَلِّينَ |
23 |
Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070023.mp3
|
الَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَاتِهِمْ دَائِمُونَ |
24 |
Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070024.mp3
|
وَالَّذِينَ فِي أَمْوَالِهِمْ حَقٌّ مَّعْلُومٌ |
25 |
Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070025.mp3
|
لِّلسَّائِلِ وَالْمَحْرُومِ |
26 |
Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070026.mp3
|
وَالَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ |
27 |
Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070027.mp3
|
وَالَّذِينَ هُم مِّنْ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشْفِقُونَ |
28 |
Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070028.mp3
|
إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمْ غَيْرُ مَأْمُونٍ |
29 |
Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070029.mp3
|
وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ |
30 |
Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070030.mp3
|
إِلَّا عَلَى أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ |
31 |
To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070031.mp3
|
فَمَنِ ابْتَغَى وَرَاء ذَلِكَ فَأُوْلَئِكَ هُمُ الْعَادُونَ |
32 |
Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070032.mp3
|
وَالَّذِينَ هُمْ لِأَمَانَاتِهِمْ وَعَهْدِهِمْ رَاعُونَ |
33 |
Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070033.mp3
|
وَالَّذِينَ هُم بِشَهَادَاتِهِمْ قَائِمُونَ |
34 |
Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070034.mp3
|
وَالَّذِينَ هُمْ عَلَى صَلَاتِهِمْ يُحَافِظُونَ |
35 |
Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne |
/content/ayah/audio/hudhaify/070035.mp3
|
أُوْلَئِكَ فِي جَنَّاتٍ مُّكْرَمُونَ |
36 |
Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu). |
/content/ayah/audio/hudhaify/070036.mp3
|
فَمَالِ الَّذِينَ كَفَرُوا قِبَلَكَ مُهْطِعِينَ |
37 |
Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a! |
/content/ayah/audio/hudhaify/070037.mp3
|
عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ عِزِينَ |
38 |
Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/070038.mp3
|
أَيَطْمَعُ كُلُّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ أَن يُدْخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ |
39 |
A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070039.mp3
|
كَلَّا إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّمَّا يَعْلَمُونَ |
40 |
Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070040.mp3
|
فَلَا أُقْسِمُ بِرَبِّ الْمَشَارِقِ وَالْمَغَارِبِ إِنَّا لَقَادِرُونَ |
41 |
Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070041.mp3
|
عَلَى أَن نُّبَدِّلَ خَيْرًا مِّنْهُمْ وَمَا نَحْنُ بِمَسْبُوقِينَ |
42 |
Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita). |
/content/ayah/audio/hudhaify/070042.mp3
|
فَذَرْهُمْ يَخُوضُوا وَيَلْعَبُوا حَتَّى يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي يُوعَدُونَ |
43 |
Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/070043.mp3
|
يَوْمَ يَخْرُجُونَ مِنَ الْأَجْدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمْ إِلَى نُصُبٍ يُوفِضُونَ |
44 |
Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa.) |
/content/ayah/audio/hudhaify/070044.mp3
|
خَاشِعَةً أَبْصَارُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ ذَلِكَ الْيَوْمُ الَّذِي كَانُوا يُوعَدُونَ |