1 |
Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068001.mp3
|
ن وَالْقَلَمِ وَمَا يَسْطُرُونَ |
2 |
Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068002.mp3
|
مَا أَنتَ بِنِعْمَةِ رَبِّكَ بِمَجْنُونٍ |
3 |
Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068003.mp3
|
وَإِنَّ لَكَ لَأَجْرًا غَيْرَ مَمْنُونٍ |
4 |
Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068004.mp3
|
وَإِنَّكَ لَعَلى خُلُقٍ عَظِيمٍ |
5 |
Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068005.mp3
|
فَسَتُبْصِرُ وَيُبْصِرُونَ |
6 |
Ga wanenku haukã take. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068006.mp3
|
بِأَييِّكُمُ الْمَفْتُونُ |
7 |
Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkinSa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068007.mp3
|
إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ |
8 |
Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068008.mp3
|
فَلَا تُطِعِ الْمُكَذِّبِينَ |
9 |
Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068009.mp3
|
وَدُّوا لَوْ تُدْهِنُ فَيُدْهِنُونَ |
10 |
Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068010.mp3
|
وَلَا تُطِعْ كُلَّ حَلَّافٍ مَّهِينٍ |
11 |
Mai zunɗe, mai yãwo da gulma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068011.mp3
|
هَمَّازٍ مَّشَّاء بِنَمِيمٍ |
12 |
Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068012.mp3
|
مَنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ |
13 |
Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri). |
/content/ayah/audio/hudhaify/068013.mp3
|
عُتُلٍّ بَعْدَ ذَلِكَ زَنِيمٍ |
14 |
Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068014.mp3
|
أَن كَانَ ذَا مَالٍ وَبَنِينَ |
15 |
Idan ana karanta masa ãyõyinMu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/068015.mp3
|
إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ |
16 |
Zã Mu yi masa alãma a kan hanci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068016.mp3
|
سَنَسِمُهُ عَلَى الْخُرْطُومِ |
17 |
Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068017.mp3
|
إِنَّا بَلَوْنَاهُمْ كَمَا بَلَوْنَا أَصْحَابَ الْجَنَّةِ إِذْ أَقْسَمُوا لَيَصْرِمُنَّهَا مُصْبِحِينَ |
18 |
Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068018.mp3
|
وَلَا يَسْتَثْنُونَ |
19 |
Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068019.mp3
|
فَطَافَ عَلَيْهَا طَائِفٌ مِّن رَّبِّكَ وَهُمْ نَائِمُونَ |
20 |
Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068020.mp3
|
فَأَصْبَحَتْ كَالصَّرِيمِ |
21 |
Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068021.mp3
|
فَتَنَادَوا مُصْبِحِينَ |
22 |
Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068022.mp3
|
أَنِ اغْدُوا عَلَى حَرْثِكُمْ إِن كُنتُمْ صَارِمِينَ |
23 |
Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa). |
/content/ayah/audio/hudhaify/068023.mp3
|
فَانطَلَقُوا وَهُمْ يَتَخَافَتُونَ |
24 |
"Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/068024.mp3
|
أَن لَّا يَدْخُلَنَّهَا الْيَوْمَ عَلَيْكُم مِّسْكِينٌ |
25 |
Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068025.mp3
|
وَغَدَوْا عَلَى حَرْدٍ قَادِرِينَ |
26 |
Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace)!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/068026.mp3
|
فَلَمَّا رَأَوْهَا قَالُوا إِنَّا لَضَالُّونَ |
27 |
"Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/068027.mp3
|
بَلْ نَحْنُ مَحْرُومُونَ |
28 |
Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/068028.mp3
|
قَالَ أَوْسَطُهُمْ أَلَمْ أَقُل لَّكُمْ لَوْلَا تُسَبِّحُونَ |
29 |
Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai." |
/content/ayah/audio/hudhaify/068029.mp3
|
قَالُوا سُبْحَانَ رَبِّنَا إِنَّا كُنَّا ظَالِمِينَ |
30 |
Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068030.mp3
|
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ يَتَلَاوَمُونَ |
31 |
Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka." |
/content/ayah/audio/hudhaify/068031.mp3
|
قَالُوا يَا وَيْلَنَا إِنَّا كُنَّا طَاغِينَ |
32 |
"Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/068032.mp3
|
عَسَى رَبُّنَا أَن يُبْدِلَنَا خَيْرًا مِّنْهَا إِنَّا إِلَى رَبِّنَا رَاغِبُونَ |
33 |
Haka dai azãbar take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068033.mp3
|
كَذَلِكَ الْعَذَابُ وَلَعَذَابُ الْآخِرَةِ أَكْبَرُ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ |
34 |
Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068034.mp3
|
إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمْ جَنَّاتِ النَّعِيمِ |
35 |
Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068035.mp3
|
أَفَنَجْعَلُ الْمُسْلِمِينَ كَالْمُجْرِمِينَ |
36 |
Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068036.mp3
|
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ |
37 |
Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068037.mp3
|
أَمْ لَكُمْ كِتَابٌ فِيهِ تَدْرُسُونَ |
38 |
Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068038.mp3
|
إِنَّ لَكُمْ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ |
39 |
Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kanMu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068039.mp3
|
أَمْ لَكُمْ أَيْمَانٌ عَلَيْنَا بَالِغَةٌ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ إِنَّ لَكُمْ لَمَا تَحْكُمُونَ |
40 |
Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068040.mp3
|
سَلْهُم أَيُّهُم بِذَلِكَ زَعِيمٌ |
41 |
Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068041.mp3
|
أَمْ لَهُمْ شُرَكَاء فَلْيَأْتُوا بِشُرَكَائِهِمْ إِن كَانُوا صَادِقِينَ |
42 |
Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujũda, sai bã zã su iyãwa ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068042.mp3
|
يَوْمَ يُكْشَفُ عَن سَاقٍ وَيُدْعَوْنَ إِلَى السُّجُودِ فَلَا يَسْتَطِيعُونَ |
43 |
Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi). |
/content/ayah/audio/hudhaify/068043.mp3
|
خَاشِعَةً أَبْصَارُهُمْ تَرْهَقُهُمْ ذِلَّةٌ وَقَدْ كَانُوا يُدْعَوْنَ إِلَى السُّجُودِ وَهُمْ سَالِمُونَ |
44 |
Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068044.mp3
|
فَذَرْنِي وَمَن يُكَذِّبُ بِهَذَا الْحَدِيثِ سَنَسْتَدْرِجُهُم مِّنْ حَيْثُ لَا يَعْلَمُونَ |
45 |
Ina jinkirtã musu, lalle kaidiNa mai ƙarfi ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068045.mp3
|
وَأُمْلِي لَهُمْ إِنَّ كَيْدِي مَتِينٌ |
46 |
Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068046.mp3
|
أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ |
47 |
Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne? |
/content/ayah/audio/hudhaify/068047.mp3
|
أَمْ عِندَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ |
48 |
Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068048.mp3
|
فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ الْحُوتِ إِذْ نَادَى وَهُوَ مَكْظُومٌ |
49 |
Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068049.mp3
|
لَوْلَا أَن تَدَارَكَهُ نِعْمَةٌ مِّن رَّبِّهِ لَنُبِذَ بِالْعَرَاء وَهُوَ مَذْمُومٌ |
50 |
Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068050.mp3
|
فَاجْتَبَاهُ رَبُّهُ فَجَعَلَهُ مِنَ الصَّالِحِينَ |
51 |
Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/068051.mp3
|
وَإِن يَكَادُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَيُزْلِقُونَكَ بِأَبْصَارِهِمْ لَمَّا سَمِعُوا الذِّكْرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُ لَمَجْنُونٌ |
52 |
Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/068052.mp3
|
وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ |