1 |
¡̃. Inã rantsuwa da Alƙur'ãni Mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050001.mp3
|
ق وَالْقُرْآنِ الْمَجِيدِ |
2 |
Ã'a, sun yi mãmãki, cewa mai gargaɗi, daga gare su, yã zo musu, sai kãfirai suka ce: "Wannan wani abu ne mai ban mãmãki." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050002.mp3
|
بَلْ عَجِبُوا أَن جَاءهُمْ مُنذِرٌ مِّنْهُمْ فَقَالَ الْكَافِرُونَ هَذَا شَيْءٌ عَجِيبٌ |
3 |
"Shin idan muka mutu kuma muka kasance turɓãya (zã a kõmo da mu)? Waccan kõmowa ce mai nĩsa." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050003.mp3
|
أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا ذَلِكَ رَجْعٌ بَعِيدٌ |
4 |
Lalle ne Mun san abin da ƙasã ke ragẽwo daga gare su, kuma wurinMu akwai wani littãfi mai tsarẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050004.mp3
|
قَدْ عَلِمْنَا مَا تَنقُصُ الْأَرْضُ مِنْهُمْ وَعِندَنَا كِتَابٌ حَفِيظٌ |
5 |
Ã'a, sun ƙaryata ne game da gaskiyar a lõkacin da ta je musu, sabõda haka sunã a cikin wani al'amari mai raurawa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050005.mp3
|
بَلْ كَذَّبُوا بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءهُمْ فَهُمْ فِي أَمْرٍ مَّرِيجٍ |
6 |
Shin, to, ba su yi dubi ba zuwa ga samã a bisa gare su, yadda Muka gĩna ta, kuma Muka ƙawãce ta, kuma bã ta da waɗansu tsãgogi? |
/content/ayah/audio/hudhaify/050006.mp3
|
أَفَلَمْ يَنظُرُوا إِلَى السَّمَاء فَوْقَهُمْ كَيْفَ بَنَيْنَاهَا وَزَيَّنَّاهَا وَمَا لَهَا مِن فُرُوجٍ |
7 |
Da ƙasã, Mun mĩƙe ta, kuma Mun jẽfa kafaffun duwãtsu a cikinta, kuma Mun tsirar, a cikinta daga kõwane ma'auri mai ban sha'awa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/050007.mp3
|
وَالْأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوْجٍ بَهِيجٍ |
8 |
Dõmin wãyar da ido da tunãtarwa ga dukan bãwa mai tawakkali? |
/content/ayah/audio/hudhaify/050008.mp3
|
تَبْصِرَةً وَذِكْرَى لِكُلِّ عَبْدٍ مُّنِيبٍ |
9 |
Kuma Mun sassakar, daga samã ruwa mai albarka sa'an nan Muka tsirar game da shi (itãcen) lambuna da ƙwãya abin girbẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050009.mp3
|
وَنَزَّلْنَا مِنَ السَّمَاء مَاء مُّبَارَكًا فَأَنبَتْنَا بِهِ جَنَّاتٍ وَحَبَّ الْحَصِيدِ |
10 |
Da itãcen dabĩno dõgãye, sunã da'ya'yan itãce gunda mãsu hauhawar jũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050010.mp3
|
وَالنَّخْلَ بَاسِقَاتٍ لَّهَا طَلْعٌ نَّضِيدٌ |
11 |
Dõmin arziki ga bãyi, kuma Muka rãyar da ƙasa matacciya game da shi. Kamar wannan ne fitar daga kabari kake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050011.mp3
|
رِزْقًا لِّلْعِبَادِ وَأَحْيَيْنَا بِهِ بَلْدَةً مَّيْتًا كَذَلِكَ الْخُرُوجُ |
12 |
Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050012.mp3
|
كَذَّبَتْ قَبْلَهُمْ قَوْمُ نُوحٍ وَأَصْحَابُ الرَّسِّ وَثَمُودُ |
13 |
Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050013.mp3
|
وَعَادٌ وَفِرْعَوْنُ وَإِخْوَانُ لُوطٍ |
14 |
Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050014.mp3
|
وَأَصْحَابُ الْأَيْكَةِ وَقَوْمُ تُبَّعٍ كُلٌّ كَذَّبَ الرُّسُلَ فَحَقَّ وَعِيدِ |
15 |
Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050015.mp3
|
أَفَعَيِينَا بِالْخَلْقِ الْأَوَّلِ بَلْ هُمْ فِي لَبْسٍ مِّنْ خَلْقٍ جَدِيدٍ |
16 |
Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050016.mp3
|
وَلَقَدْ خَلَقْنَا الْإِنسَانَ وَنَعْلَمُ مَا تُوَسْوِسُ بِهِ نَفْسُهُ وَنَحْنُ أَقْرَبُ إِلَيْهِ مِنْ حَبْلِ الْوَرِيدِ |
17 |
A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050017.mp3
|
إِذْ يَتَلَقَّى الْمُتَلَقِّيَانِ عَنِ الْيَمِينِ وَعَنِ الشِّمَالِ قَعِيدٌ |
18 |
Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050018.mp3
|
مَا يَلْفِظُ مِن قَوْلٍ إِلَّا لَدَيْهِ رَقِيبٌ عَتِيدٌ |
19 |
Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050019.mp3
|
وَجَاءتْ سَكْرَةُ الْمَوْتِ بِالْحَقِّ ذَلِكَ مَا كُنتَ مِنْهُ تَحِيدُ |
20 |
Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050020.mp3
|
وَنُفِخَ فِي الصُّورِ ذَلِكَ يَوْمُ الْوَعِيدِ |
21 |
Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050021.mp3
|
وَجَاءتْ كُلُّ نَفْسٍ مَّعَهَا سَائِقٌ وَشَهِيدٌ |
22 |
(Sai a ce masa): "Lalle ne, haƙĩƙa, ka kasance a cikin gafala daga wannan. To, Mun kuranye maka rufinka, sabõda haka ganinka a yau, mai kaifi ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050022.mp3
|
لَقَدْ كُنتَ فِي غَفْلَةٍ مِّنْ هَذَا فَكَشَفْنَا عَنكَ غِطَاءكَ فَبَصَرُكَ الْيَوْمَ حَدِيدٌ |
23 |
Kuma abõkin haɗinsa ya ce: "Wannan shi ne abin da ke tãre da ni halarce." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050023.mp3
|
وَقَالَ قَرِينُهُ هَذَا مَا لَدَيَّ عَتِيدٌ |
24 |
(A ce wa Malã'iku), "Ku jẽfa, a cikin Jahannama, dukan mai yawan kãfirci, mai tsaurin rai." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050024.mp3
|
أَلْقِيَا فِي جَهَنَّمَ كُلَّ كَفَّارٍ عَنِيدٍ |
25 |
"Mai yawan hanãwa ga alhẽri, mai zãlunci, mai shakka." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050025.mp3
|
مَّنَّاعٍ لِّلْخَيْرِ مُعْتَدٍ مُّرِيبٍ |
26 |
"Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050026.mp3
|
الَّذِي جَعَلَ مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ فَأَلْقِيَاهُ فِي الْعَذَابِ الشَّدِيدِ |
27 |
Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050027.mp3
|
قَالَ قَرِينُهُ رَبَّنَا مَا أَطْغَيْتُهُ وَلَكِن كَانَ فِي ضَلَالٍ بَعِيدٍ |
28 |
Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050028.mp3
|
قَالَ لَا تَخْتَصِمُوا لَدَيَّ وَقَدْ قَدَّمْتُ إِلَيْكُم بِالْوَعِيدِ |
29 |
"Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050029.mp3
|
مَا يُبَدَّلُ الْقَوْلُ لَدَيَّ وَمَا أَنَا بِظَلَّامٍ لِّلْعَبِيدِ |
30 |
Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/050030.mp3
|
يَوْمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ امْتَلَأْتِ وَتَقُولُ هَلْ مِن مَّزِيدٍ |
31 |
Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050031.mp3
|
وَأُزْلِفَتِ الْجَنَّةُ لِلْمُتَّقِينَ غَيْرَ بَعِيدٍ |
32 |
"Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa). |
/content/ayah/audio/hudhaify/050032.mp3
|
هَذَا مَا تُوعَدُونَ لِكُلِّ أَوَّابٍ حَفِيظٍ |
33 |
"Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050033.mp3
|
مَنْ خَشِيَ الرَّحْمَن بِالْغَيْبِ وَجَاء بِقَلْبٍ مُّنِيبٍ |
34 |
(A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama." |
/content/ayah/audio/hudhaify/050034.mp3
|
ادْخُلُوهَا بِسَلَامٍ ذَلِكَ يَوْمُ الْخُلُودِ |
35 |
Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima, |
/content/ayah/audio/hudhaify/050035.mp3
|
لَهُم مَّا يَشَاؤُونَ فِيهَا وَلَدَيْنَا مَزِيدٌ |
36 |
Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu). |
/content/ayah/audio/hudhaify/050036.mp3
|
وَكَمْ أَهْلَكْنَا قَبْلَهُم مِّن قَرْنٍ هُمْ أَشَدُّ مِنْهُم بَطْشًا فَنَقَّبُوا فِي الْبِلَادِ هَلْ مِن مَّحِيصٍ |
37 |
Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa). |
/content/ayah/audio/hudhaify/050037.mp3
|
إِنَّ فِي ذَلِكَ لَذِكْرَى لِمَن كَانَ لَهُ قَلْبٌ أَوْ أَلْقَى السَّمْعَ وَهُوَ شَهِيدٌ |
38 |
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050038.mp3
|
وَلَقَدْ خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَمَا مَسَّنَا مِن لُّغُوبٍ |
39 |
Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050039.mp3
|
فَاصْبِرْ عَلَى مَا يَقُولُونَ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ الْغُرُوبِ |
40 |
Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050040.mp3
|
وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَأَدْبَارَ السُّجُودِ |
41 |
Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050041.mp3
|
وَاسْتَمِعْ يَوْمَ يُنَادِ الْمُنَادِ مِن مَّكَانٍ قَرِيبٍ |
42 |
Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari). |
/content/ayah/audio/hudhaify/050042.mp3
|
يَوْمَ يَسْمَعُونَ الصَّيْحَةَ بِالْحَقِّ ذَلِكَ يَوْمُ الْخُرُوجِ |
43 |
Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050043.mp3
|
إِنَّا نَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَإِلَيْنَا الْمَصِيرُ |
44 |
Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050044.mp3
|
يَوْمَ تَشَقَّقُ الْأَرْضُ عَنْهُمْ سِرَاعًا ذَلِكَ حَشْرٌ عَلَيْنَا يَسِيرٌ |
45 |
Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/050045.mp3
|
نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَا يَقُولُونَ وَمَا أَنتَ عَلَيْهِم بِجَبَّارٍ فَذَكِّرْ بِالْقُرْآنِ مَن يَخَافُ وَعِيدِ |