1 |
Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051001.mp3
|
وَالذَّارِيَاتِ ذَرْوًا |
2 |
Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051002.mp3
|
فَالْحَامِلَاتِ وِقْرًا |
3 |
Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051003.mp3
|
فَالْجَارِيَاتِ يُسْرًا |
4 |
Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051004.mp3
|
فَالْمُقَسِّمَاتِ أَمْرًا |
5 |
Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051005.mp3
|
إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَصَادِقٌ |
6 |
Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne |
/content/ayah/audio/hudhaify/051006.mp3
|
وَإِنَّ الدِّينَ لَوَاقِعٌ |
7 |
Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051007.mp3
|
وَالسَّمَاء ذَاتِ الْحُبُكِ |
8 |
Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051008.mp3
|
إِنَّكُمْ لَفِي قَوْلٍ مُّخْتَلِفٍ |
9 |
Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051009.mp3
|
يُؤْفَكُ عَنْهُ مَنْ أُفِكَ |
10 |
An la'ani mãsu ƙiri-faɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051010.mp3
|
قُتِلَ الْخَرَّاصُونَ |
11 |
Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051011.mp3
|
الَّذِينَ هُمْ فِي غَمْرَةٍ سَاهُونَ |
12 |
Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/051012.mp3
|
يَسْأَلُونَ أَيَّانَ يَوْمُ الدِّينِ |
13 |
Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051013.mp3
|
يَوْمَ هُمْ عَلَى النَّارِ يُفْتَنُونَ |
14 |
(A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa." |
/content/ayah/audio/hudhaify/051014.mp3
|
ذُوقُوا فِتْنَتَكُمْ هَذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تَسْتَعْجِلُونَ |
15 |
Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051015.mp3
|
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ |
16 |
Sunã mãsu dĩbar abin da Ubangijinsu Ya bã su. Lalle sũ, sun kasance mãsu kyautatãwa a gabãnin haka (a dũniya). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051016.mp3
|
آخِذِينَ مَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ إِنَّهُمْ كَانُوا قَبْلَ ذَلِكَ مُحْسِنِينَ |
17 |
Sun kasance a lõkaci kaɗan na dare suke yin barci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051017.mp3
|
كَانُوا قَلِيلًا مِّنَ اللَّيْلِ مَا يَهْجَعُونَ |
18 |
Kuma a lõkutan asuba sunã ta yin istigfãri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051018.mp3
|
وَبِالْأَسْحَارِ هُمْ يَسْتَغْفِرُونَ |
19 |
Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051019.mp3
|
وَفِي أَمْوَالِهِمْ حَقٌّ لِّلسَّائِلِ وَالْمَحْرُومِ |
20 |
Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051020.mp3
|
وَفِي الْأَرْضِ آيَاتٌ لِّلْمُوقِنِينَ |
21 |
Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/051021.mp3
|
وَفِي أَنفُسِكُمْ أَفَلَا تُبْصِرُونَ |
22 |
Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051022.mp3
|
وَفِي السَّمَاء رِزْقُكُمْ وَمَا تُوعَدُونَ |
23 |
To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana, |
/content/ayah/audio/hudhaify/051023.mp3
|
فَوَرَبِّ السَّمَاء وَالْأَرْضِ إِنَّهُ لَحَقٌّ مِّثْلَ مَا أَنَّكُمْ تَنطِقُونَ |
24 |
Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka? |
/content/ayah/audio/hudhaify/051024.mp3
|
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ ضَيْفِ إِبْرَاهِيمَ الْمُكْرَمِينَ |
25 |
A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/051025.mp3
|
إِذْ دَخَلُوا عَلَيْهِ فَقَالُوا سَلَامًا قَالَ سَلَامٌ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ |
26 |
Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna, |
/content/ayah/audio/hudhaify/051026.mp3
|
فَرَاغَ إِلَى أَهْلِهِ فَجَاء بِعِجْلٍ سَمِينٍ |
27 |
Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/051027.mp3
|
فَقَرَّبَهُ إِلَيْهِمْ قَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ |
28 |
Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051028.mp3
|
فَأَوْجَسَ مِنْهُمْ خِيفَةً قَالُوا لَا تَخَفْ وَبَشَّرُوهُ بِغُلَامٍ عَلِيمٍ |
29 |
Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/051029.mp3
|
فَأَقْبَلَتِ امْرَأَتُهُ فِي صَرَّةٍ فَصَكَّتْ وَجْهَهَا وَقَالَتْ عَجُوزٌ عَقِيمٌ |
30 |
Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/051030.mp3
|
قَالُوا كَذَلِكَ قَالَ رَبُّكِ إِنَّهُ هُوَ الْحَكِيمُ الْعَلِيمُ |
31 |
(Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/051031.mp3
|
قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ |
32 |
Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051032.mp3
|
قَالُوا إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَى قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ |
33 |
"Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom). |
/content/ayah/audio/hudhaify/051033.mp3
|
لِنُرْسِلَ عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن طِينٍ |
34 |
"Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna." |
/content/ayah/audio/hudhaify/051034.mp3
|
مُسَوَّمَةً عِندَ رَبِّكَ لِلْمُسْرِفِينَ |
35 |
Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051035.mp3
|
فَأَخْرَجْنَا مَن كَانَ فِيهَا مِنَ الْمُؤْمِنِينَ |
36 |
Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051036.mp3
|
فَمَا وَجَدْنَا فِيهَا غَيْرَ بَيْتٍ مِّنَ الْمُسْلِمِينَ |
37 |
Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051037.mp3
|
وَتَرَكْنَا فِيهَا آيَةً لِّلَّذِينَ يَخَافُونَ الْعَذَابَ الْأَلِيمَ |
38 |
Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051038.mp3
|
وَفِي مُوسَى إِذْ أَرْسَلْنَاهُ إِلَى فِرْعَوْنَ بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ |
39 |
Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/051039.mp3
|
فَتَوَلَّى بِرُكْنِهِ وَقَالَ سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ |
40 |
Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051040.mp3
|
فَأَخَذْنَاهُ وَجُنُودَهُ فَنَبَذْنَاهُمْ فِي الْيَمِّ وَهُوَ مُلِيمٌ |
41 |
Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051041.mp3
|
وَفِي عَادٍ إِذْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِمُ الرِّيحَ الْعَقِيمَ |
42 |
Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051042.mp3
|
مَا تَذَرُ مِن شَيْءٍ أَتَتْ عَلَيْهِ إِلَّا جَعَلَتْهُ كَالرَّمِيمِ |
43 |
Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci," |
/content/ayah/audio/hudhaify/051043.mp3
|
وَفِي ثَمُودَ إِذْ قِيلَ لَهُمْ تَمَتَّعُوا حَتَّى حِينٍ |
44 |
Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051044.mp3
|
فَعَتَوْا عَنْ أَمْرِ رَبِّهِمْ فَأَخَذَتْهُمُ الصَّاعِقَةُ وَهُمْ يَنظُرُونَ |
45 |
Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051045.mp3
|
فَمَا اسْتَطَاعُوا مِن قِيَامٍ وَمَا كَانُوا مُنتَصِرِينَ |
46 |
Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051046.mp3
|
وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمًا فَاسِقِينَ |
47 |
Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051047.mp3
|
وَالسَّمَاء بَنَيْنَاهَا بِأَيْدٍ وَإِنَّا لَمُوسِعُونَ |
48 |
Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ, |
/content/ayah/audio/hudhaify/051048.mp3
|
وَالْأَرْضَ فَرَشْنَاهَا فَنِعْمَ الْمَاهِدُونَ |
49 |
Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051049.mp3
|
وَمِن كُلِّ شَيْءٍ خَلَقْنَا زَوْجَيْنِ لَعَلَّكُمْ تَذَكَّرُونَ |
50 |
Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051050.mp3
|
فَفِرُّوا إِلَى اللَّهِ إِنِّي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ |
51 |
Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051051.mp3
|
وَلَا تَجْعَلُوا مَعَ اللَّهِ إِلَهًا آخَرَ إِنِّي لَكُم مِّنْهُ نَذِيرٌ مُّبِينٌ |
52 |
Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci." |
/content/ayah/audio/hudhaify/051052.mp3
|
كَذَلِكَ مَا أَتَى الَّذِينَ مِن قَبْلِهِم مِّن رَّسُولٍ إِلَّا قَالُوا سَاحِرٌ أَوْ مَجْنُونٌ |
53 |
shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051053.mp3
|
أَتَوَاصَوْا بِهِ بَلْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ |
54 |
Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051054.mp3
|
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ فَمَا أَنتَ بِمَلُومٍ |
55 |
Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051055.mp3
|
وَذَكِّرْ فَإِنَّ الذِّكْرَى تَنفَعُ الْمُؤْمِنِينَ |
56 |
Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051056.mp3
|
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ |
57 |
Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051057.mp3
|
مَا أُرِيدُ مِنْهُم مِّن رِّزْقٍ وَمَا أُرِيدُ أَن يُطْعِمُونِ |
58 |
Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051058.mp3
|
إِنَّ اللَّهَ هُوَ الرَّزَّاقُ ذُو الْقُوَّةِ الْمَتِينُ |
59 |
To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051059.mp3
|
فَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا ذَنُوبًا مِّثْلَ ذَنُوبِ أَصْحَابِهِمْ فَلَا يَسْتَعْجِلُونِ |
60 |
Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/051060.mp3
|
فَوَيْلٌ لِّلَّذِينَ كَفَرُوا مِن يَوْمِهِمُ الَّذِي يُوعَدُونَ |