Al-Qari'a

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro)! الْقَارِعَةُ
2 Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa? مَا الْقَارِعَةُ
3 Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa? وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ
4 Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa. يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ
5 Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe. وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنفُوشِ
6 To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi. فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ
7 To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda. فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ
8 Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi). وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ
9 To, uwarsa Hãwiya ce. فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ
10 Kuma me ya sanar da kai mece ce ita? وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ
11 Wata wuta ce mai zafi. نَارٌ حَامِيَةٌ
;