At-Takathur

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Alfahari da yawan dũkiya da dangi ya shagaltar da ku (dagaibada mai amfaninku). أَلْهَاكُمُ التَّكَاثُرُ
2 Har kuka ziyarci kaburbura. حَتَّى زُرْتُمُ الْمَقَابِرَ
3 A'aha! (Nan gaba) zã ku sani. كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ
4 Sa'an nan, tabbas, zã ku sani. ثُمَّ كَلَّا سَوْفَ تَعْلَمُونَ
5 Haƙĩƙa, da kuna da sani sani na yaƙĩni. كَلَّا لَوْ تَعْلَمُونَ عِلْمَ الْيَقِينِ
6 Lalle ne da kuna ganin Jahĩm. لَتَرَوُنَّ الْجَحِيمَ
7 Sa'an nan lalle ne za ku gan ta, da idanu, bayyane. ثُمَّ لَتَرَوُنَّهَا عَيْنَ الْيَقِينِ
8 Sa'an nan lalle ne za a tambaye ku, a rãnar nan lãbãrin ni'imar (da aka yi muku). ثُمَّ لَتُسْأَلُنَّ يَوْمَئِذٍ عَنِ النَّعِيمِ
;