1 |
Bã sai Nã yi rantsuwa da Rãnar ¡iyãma ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075001.mp3
|
لَا أُقْسِمُ بِيَوْمِ الْقِيَامَةِ |
2 |
Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin kansa ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075002.mp3
|
وَلَا أُقْسِمُ بِالنَّفْسِ اللَّوَّامَةِ |
3 |
Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/075003.mp3
|
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَلَّن نَجْمَعَ عِظَامَهُ |
4 |
Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075004.mp3
|
بَلَى قَادِرِينَ عَلَى أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُ |
5 |
Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075005.mp3
|
بَلْ يُرِيدُ الْإِنسَانُ لِيَفْجُرَ أَمَامَهُ |
6 |
Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/075006.mp3
|
يَسْأَلُ أَيَّانَ يَوْمُ الْقِيَامَةِ |
7 |
To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli). |
/content/ayah/audio/hudhaify/075007.mp3
|
فَإِذَا بَرِقَ الْبَصَرُ |
8 |
Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe). |
/content/ayah/audio/hudhaify/075008.mp3
|
وَخَسَفَ الْقَمَرُ |
9 |
Aka tãra rãnã da watã |
/content/ayah/audio/hudhaify/075009.mp3
|
وَجُمِعَ الشَّمْسُ وَالْقَمَرُ |
10 |
Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/075010.mp3
|
يَقُولُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ أَيْنَ الْمَفَرُّ |
11 |
A'aha! bãbu mafaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075011.mp3
|
كَلَّا لَا وَزَرَ |
12 |
zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075012.mp3
|
إِلَى رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمُسْتَقَرُّ |
13 |
Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075013.mp3
|
يُنَبَّأُ الْإِنسَانُ يَوْمَئِذٍ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ |
14 |
Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075014.mp3
|
بَلِ الْإِنسَانُ عَلَى نَفْسِهِ بَصِيرَةٌ |
15 |
Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba). |
/content/ayah/audio/hudhaify/075015.mp3
|
وَلَوْ أَلْقَى مَعَاذِيرَهُ |
16 |
Kada ka mõtsar da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni). |
/content/ayah/audio/hudhaify/075016.mp3
|
لَا تُحَرِّكْ بِهِ لِسَانَكَ لِتَعْجَلَ بِهِ |
17 |
Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075017.mp3
|
إِنَّ عَلَيْنَا جَمْعَهُ وَقُرْآنَهُ |
18 |
To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075018.mp3
|
فَإِذَا قَرَأْنَاهُ فَاتَّبِعْ قُرْآنَهُ |
19 |
sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075019.mp3
|
ثُمَّ إِنَّ عَلَيْنَا بَيَانَهُ |
20 |
A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075020.mp3
|
كَلَّا بَلْ تُحِبُّونَ الْعَاجِلَةَ |
21 |
Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira). |
/content/ayah/audio/hudhaify/075021.mp3
|
وَتَذَرُونَ الْآخِرَةَ |
22 |
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075022.mp3
|
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ |
23 |
Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075023.mp3
|
إِلَى رَبِّهَا نَاظِرَةٌ |
24 |
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075024.mp3
|
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ بَاسِرَةٌ |
25 |
Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075025.mp3
|
تَظُنُّ أَن يُفْعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ |
26 |
A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075026.mp3
|
كَلَّا إِذَا بَلَغَتْ التَّرَاقِيَ |
27 |
kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/075027.mp3
|
وَقِيلَ مَنْ رَاقٍ |
28 |
Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075028.mp3
|
وَظَنَّ أَنَّهُ الْفِرَاقُ |
29 |
Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075029.mp3
|
وَالْتَفَّتِ السَّاقُ بِالسَّاقِ |
30 |
Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa take. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075030.mp3
|
إِلَى رَبِّكَ يَوْمَئِذٍ الْمَسَاقُ |
31 |
To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba! |
/content/ayah/audio/hudhaify/075031.mp3
|
فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّى |
32 |
Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya! |
/content/ayah/audio/hudhaify/075032.mp3
|
وَلَكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّى |
33 |
Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075033.mp3
|
ثُمَّ ذَهَبَ إِلَى أَهْلِهِ يَتَمَطَّى |
34 |
Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075034.mp3
|
أَوْلَى لَكَ فَأَوْلَى |
35 |
Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/075035.mp3
|
ثُمَّ أَوْلَى لَكَ فَأَوْلَى |
36 |
Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/075036.mp3
|
أَيَحْسَبُ الْإِنسَانُ أَن يُتْرَكَ سُدًى |
37 |
Bai kasance iɗgo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) |
/content/ayah/audio/hudhaify/075037.mp3
|
أَلَمْ يَكُ نُطْفَةً مِّن مَّنِيٍّ يُمْنَى |
38 |
Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa; |
/content/ayah/audio/hudhaify/075038.mp3
|
ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّى |
39 |
Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace? |
/content/ayah/audio/hudhaify/075039.mp3
|
فَجَعَلَ مِنْهُ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَى |
40 |
Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu? |
/content/ayah/audio/hudhaify/075040.mp3
|
أَلَيْسَ ذَلِكَ بِقَادِرٍ عَلَى أَن يُحْيِيَ الْمَوْتَى |