1 |
Ḥ. M̃. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044001.mp3
|
حم |
2 |
Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044002.mp3
|
وَالْكِتَابِ الْمُبِينِ |
3 |
Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044003.mp3
|
إِنَّا أَنزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةٍ مُّبَارَكَةٍ إِنَّا كُنَّا مُنذِرِينَ |
4 |
A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044004.mp3
|
فِيهَا يُفْرَقُ كُلُّ أَمْرٍ حَكِيمٍ |
5 |
Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044005.mp3
|
أَمْرًا مِّنْ عِندِنَا إِنَّا كُنَّا مُرْسِلِينَ |
6 |
Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044006.mp3
|
رَحْمَةً مِّن رَّبِّكَ إِنَّهُ هُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ |
7 |
(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). |
/content/ayah/audio/hudhaify/044007.mp3
|
رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ |
8 |
Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044008.mp3
|
لَا إِلَهَ إِلَّا هُوَ يُحْيِي وَيُمِيتُ رَبُّكُمْ وَرَبُّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ |
9 |
A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044009.mp3
|
بَلْ هُمْ فِي شَكٍّ يَلْعَبُونَ |
10 |
Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044010.mp3
|
فَارْتَقِبْ يَوْمَ تَأْتِي السَّمَاء بِدُخَانٍ مُّبِينٍ |
11 |
Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044011.mp3
|
يَغْشَى النَّاسَ هَذَا عَذَابٌ أَلِيمٌ |
12 |
Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044012.mp3
|
رَبَّنَا اكْشِفْ عَنَّا الْعَذَابَ إِنَّا مُؤْمِنُونَ |
13 |
Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/044013.mp3
|
أَنَّى لَهُمُ الذِّكْرَى وَقَدْ جَاءهُمْ رَسُولٌ مُّبِينٌ |
14 |
Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044014.mp3
|
ثُمَّ تَوَلَّوْا عَنْهُ وَقَالُوا مُعَلَّمٌ مَّجْنُونٌ |
15 |
Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). |
/content/ayah/audio/hudhaify/044015.mp3
|
إِنَّا كَاشِفُو الْعَذَابِ قَلِيلًا إِنَّكُمْ عَائِدُونَ |
16 |
Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044016.mp3
|
يَوْمَ نَبْطِشُ الْبَطْشَةَ الْكُبْرَى إِنَّا مُنتَقِمُونَ |
17 |
Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044017.mp3
|
وَلَقَدْ فَتَنَّا قَبْلَهُمْ قَوْمَ فِرْعَوْنَ وَجَاءهُمْ رَسُولٌ كَرِيمٌ |
18 |
(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044018.mp3
|
أَنْ أَدُّوا إِلَيَّ عِبَادَ اللَّهِ إِنِّي لَكُمْ رَسُولٌ أَمِينٌ |
19 |
"Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044019.mp3
|
وَأَنْ لَّا تَعْلُوا عَلَى اللَّهِ إِنِّي آتِيكُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ |
20 |
"Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044020.mp3
|
وَإِنِّي عُذْتُ بِرَبِّي وَرَبِّكُمْ أَن تَرْجُمُونِ |
21 |
"Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044021.mp3
|
وَإِنْ لَّمْ تُؤْمِنُوا لِي فَاعْتَزِلُونِ |
22 |
Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044022.mp3
|
فَدَعَا رَبَّهُ أَنَّ هَؤُلَاء قَوْمٌ مُّجْرِمُونَ |
23 |
(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" |
/content/ayah/audio/hudhaify/044023.mp3
|
فَأَسْرِ بِعِبَادِي لَيْلًا إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ |
24 |
"Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044024.mp3
|
وَاتْرُكْ الْبَحْرَ رَهْوًا إِنَّهُمْ جُندٌ مُّغْرَقُونَ |
25 |
Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044025.mp3
|
كَمْ تَرَكُوا مِن جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ |
26 |
Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044026.mp3
|
وَزُرُوعٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ |
27 |
Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044027.mp3
|
وَنَعْمَةٍ كَانُوا فِيهَا فَاكِهِينَ |
28 |
Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044028.mp3
|
كَذَلِكَ وَأَوْرَثْنَاهَا قَوْمًا آخَرِينَ |
29 |
Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044029.mp3
|
فَمَا بَكَتْ عَلَيْهِمُ السَّمَاء وَالْأَرْضُ وَمَا كَانُوا مُنظَرِينَ |
30 |
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044030.mp3
|
وَلَقَدْ نَجَّيْنَا بَنِي إِسْرَائِيلَ مِنَ الْعَذَابِ الْمُهِينِ |
31 |
Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044031.mp3
|
مِن فِرْعَوْنَ إِنَّهُ كَانَ عَالِيًا مِّنَ الْمُسْرِفِينَ |
32 |
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044032.mp3
|
وَلَقَدِ اخْتَرْنَاهُمْ عَلَى عِلْمٍ عَلَى الْعَالَمِينَ |
33 |
Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna |
/content/ayah/audio/hudhaify/044033.mp3
|
وَآتَيْنَاهُم مِّنَ الْآيَاتِ مَا فِيهِ بَلَاء مُّبِينٌ |
34 |
Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/044034.mp3
|
إِنَّ هَؤُلَاء لَيَقُولُونَ |
35 |
"Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044035.mp3
|
إِنْ هِيَ إِلَّا مَوْتَتُنَا الْأُولَى وَمَا نَحْنُ بِمُنشَرِينَ |
36 |
"Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044036.mp3
|
فَأْتُوا بِآبَائِنَا إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ |
37 |
shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044037.mp3
|
أَهُمْ خَيْرٌ أَمْ قَوْمُ تُبَّعٍ وَالَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ أَهْلَكْنَاهُمْ إِنَّهُمْ كَانُوا مُجْرِمِينَ |
38 |
Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044038.mp3
|
وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا لَاعِبِينَ |
39 |
Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044039.mp3
|
مَا خَلَقْنَاهُمَا إِلَّا بِالْحَقِّ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ |
40 |
Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044040.mp3
|
إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ مِيقَاتُهُمْ أَجْمَعِينَ |
41 |
Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044041.mp3
|
يَوْمَ لَا يُغْنِي مَوْلًى عَن مَّوْلًى شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ |
42 |
fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044042.mp3
|
إِلَّا مَن رَّحِمَ اللَّهُ إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ |
43 |
Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), |
/content/ayah/audio/hudhaify/044043.mp3
|
إِنَّ شَجَرَةَ الزَّقُّومِ |
44 |
Ita ce abincin mai laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044044.mp3
|
طَعَامُ الْأَثِيمِ |
45 |
Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044045.mp3
|
كَالْمُهْلِ يَغْلِي فِي الْبُطُونِ |
46 |
Kamar tafasar ruwan zãfi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044046.mp3
|
كَغَلْيِ الْحَمِيمِ |
47 |
(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044047.mp3
|
خُذُوهُ فَاعْتِلُوهُ إِلَى سَوَاء الْجَحِيمِ |
48 |
"Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044048.mp3
|
ثُمَّ صُبُّوا فَوْقَ رَأْسِهِ مِنْ عَذَابِ الْحَمِيمِ |
49 |
(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/044049.mp3
|
ذُقْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْكَرِيمُ |
50 |
"Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/044050.mp3
|
إِنَّ هَذَا مَا كُنتُم بِهِ تَمْتَرُونَ |
51 |
Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044051.mp3
|
إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي مَقَامٍ أَمِينٍ |
52 |
A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044052.mp3
|
فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ |
53 |
Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044053.mp3
|
يَلْبَسُونَ مِن سُندُسٍ وَإِسْتَبْرَقٍ مُّتَقَابِلِينَ |
54 |
Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044054.mp3
|
كَذَلِكَ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ |
55 |
Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). |
/content/ayah/audio/hudhaify/044055.mp3
|
يَدْعُونَ فِيهَا بِكُلِّ فَاكِهَةٍ آمِنِينَ |
56 |
Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044056.mp3
|
لَا يَذُوقُونَ فِيهَا الْمَوْتَ إِلَّا الْمَوْتَةَ الْأُولَى وَوَقَاهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ |
57 |
Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044057.mp3
|
فَضْلًا مِّن رَّبِّكَ ذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ |
58 |
Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044058.mp3
|
فَإِنَّمَا يَسَّرْنَاهُ بِلِسَانِكَ لَعَلَّهُمْ يَتَذَكَّرُونَ |
59 |
Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/044059.mp3
|
فَارْتَقِبْ إِنَّهُم مُّرْتَقِبُونَ |