1 |
Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi). |
/content/ayah/audio/hudhaify/037001.mp3
|
وَالصَّافَّاتِ صَفًّا |
2 |
Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037002.mp3
|
فَالزَّاجِرَاتِ زَجْرًا |
3 |
Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037003.mp3
|
فَالتَّالِيَاتِ ذِكْرًا |
4 |
Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037004.mp3
|
إِنَّ إِلَهَكُمْ لَوَاحِدٌ |
5 |
Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037005.mp3
|
رَبُّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَرَبُّ الْمَشَارِقِ |
6 |
Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037006.mp3
|
إِنَّا زَيَّنَّا السَّمَاء الدُّنْيَا بِزِينَةٍ الْكَوَاكِبِ |
7 |
Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037007.mp3
|
وَحِفْظًا مِّن كُلِّ شَيْطَانٍ مَّارِدٍ |
8 |
Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037008.mp3
|
لَا يَسَّمَّعُونَ إِلَى الْمَلَإِ الْأَعْلَى وَيُقْذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ |
9 |
Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037009.mp3
|
دُحُورًا وَلَهُمْ عَذَابٌ وَاصِبٌ |
10 |
Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037010.mp3
|
إِلَّا مَنْ خَطِفَ الْخَطْفَةَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ ثَاقِبٌ |
11 |
Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037011.mp3
|
فَاسْتَفْتِهِمْ أَهُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَم مَّنْ خَلَقْنَا إِنَّا خَلَقْنَاهُم مِّن طِينٍ لَّازِبٍ |
12 |
Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037012.mp3
|
بَلْ عَجِبْتَ وَيَسْخَرُونَ |
13 |
Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037013.mp3
|
وَإِذَا ذُكِّرُوا لَا يَذْكُرُونَ |
14 |
Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037014.mp3
|
وَإِذَا رَأَوْا آيَةً يَسْتَسْخِرُونَ |
15 |
Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037015.mp3
|
وَقَالُوا إِنْ هَذَا إِلَّا سِحْرٌ مُّبِينٌ |
16 |
"Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037016.mp3
|
أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَئِنَّا لَمَبْعُوثُونَ |
17 |
"Ashe kõ da ubanninmu na farko?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037017.mp3
|
أَوَآبَاؤُنَا الْأَوَّلُونَ |
18 |
Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037018.mp3
|
قُلْ نَعَمْ وَأَنتُمْ دَاخِرُونَ |
19 |
Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037019.mp3
|
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ فَإِذَا هُمْ يَنظُرُونَ |
20 |
Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037020.mp3
|
وَقَالُوا يَا وَيْلَنَا هَذَا يَوْمُ الدِّينِ |
21 |
Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037021.mp3
|
هَذَا يَوْمُ الْفَصْلِ الَّذِي كُنتُمْ بِهِ تُكَذِّبُونَ |
22 |
Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037022.mp3
|
احْشُرُوا الَّذِينَ ظَلَمُوا وَأَزْوَاجَهُمْ وَمَا كَانُوا يَعْبُدُونَ |
23 |
Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037023.mp3
|
مِن دُونِ اللَّهِ فَاهْدُوهُمْ إِلَى صِرَاطِ الْجَحِيمِ |
24 |
Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037024.mp3
|
وَقِفُوهُمْ إِنَّهُم مَّسْئُولُونَ |
25 |
Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037025.mp3
|
مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ |
26 |
Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037026.mp3
|
بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ |
27 |
Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037027.mp3
|
وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ يَتَسَاءلُونَ |
28 |
Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037028.mp3
|
قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِ |
29 |
Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037029.mp3
|
قَالُوا بَل لَّمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَ |
30 |
"Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037030.mp3
|
وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَانٍ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَاغِينَ |
31 |
"Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037031.mp3
|
فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا إِنَّا لَذَائِقُونَ |
32 |
"Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037032.mp3
|
فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ |
33 |
To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037033.mp3
|
فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ |
34 |
Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037034.mp3
|
إِنَّا كَذَلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ |
35 |
Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037035.mp3
|
إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ |
36 |
Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037036.mp3
|
وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوا آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍ |
37 |
Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037037.mp3
|
بَلْ جَاء بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ |
38 |
Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037038.mp3
|
إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الْأَلِيمِ |
39 |
Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037039.mp3
|
وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ |
40 |
Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037040.mp3
|
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ |
41 |
Waɗannan sunã da abinci sananne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037041.mp3
|
أُوْلَئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ |
42 |
'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037042.mp3
|
فَوَاكِهُ وَهُم مُّكْرَمُونَ |
43 |
A cikin gidãjen Aljannar ni'ima. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037043.mp3
|
فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ |
44 |
A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037044.mp3
|
عَلَى سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَ |
45 |
Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037045.mp3
|
يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِن مَّعِينٍ |
46 |
Farã mai dãɗi ga mashãyan. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037046.mp3
|
بَيْضَاء لَذَّةٍ لِّلشَّارِبِينَ |
47 |
A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba, |
/content/ayah/audio/hudhaify/037047.mp3
|
لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ |
48 |
Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037048.mp3
|
وَعِنْدَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌ |
49 |
Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037049.mp3
|
كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ |
50 |
Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037050.mp3
|
فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَى بَعْضٍ يَتَسَاءلُونَ |
51 |
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037051.mp3
|
قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌ |
52 |
Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037052.mp3
|
يَقُولُ أَئِنَّكَ لَمِنْ الْمُصَدِّقِينَ |
53 |
"Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037053.mp3
|
أَئِذَا مِتْنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَامًا أَئِنَّا لَمَدِينُونَ |
54 |
(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037054.mp3
|
قَالَ هَلْ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ |
55 |
Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037055.mp3
|
فَاطَّلَعَ فَرَآهُ فِي سَوَاء الْجَحِيمِ |
56 |
Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037056.mp3
|
قَالَ تَاللَّهِ إِنْ كِدتَّ لَتُرْدِينِ |
57 |
"Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037057.mp3
|
وَلَوْلَا نِعْمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ الْمُحْضَرِينَ |
58 |
"Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037058.mp3
|
أَفَمَا نَحْنُ بِمَيِّتِينَ |
59 |
"Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037059.mp3
|
إِلَّا مَوْتَتَنَا الْأُولَى وَمَا نَحْنُ بِمُعَذَّبِينَ |
60 |
Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037060.mp3
|
إِنَّ هَذَا لَهُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ |
61 |
Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037061.mp3
|
لِمِثْلِ هَذَا فَلْيَعْمَلْ الْعَامِلُونَ |
62 |
Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037062.mp3
|
أَذَلِكَ خَيْرٌ نُّزُلًا أَمْ شَجَرَةُ الزَّقُّومِ |
63 |
Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037063.mp3
|
إِنَّا جَعَلْنَاهَا فِتْنَةً لِّلظَّالِمِينَ |
64 |
Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037064.mp3
|
إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخْرُجُ فِي أَصْلِ الْجَحِيمِ |
65 |
Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037065.mp3
|
طَلْعُهَا كَأَنَّهُ رُؤُوسُ الشَّيَاطِينِ |
66 |
To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037066.mp3
|
فَإِنَّهُمْ لَآكِلُونَ مِنْهَا فَمَالِؤُونَ مِنْهَا الْبُطُونَ |
67 |
Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037067.mp3
|
ثُمَّ إِنَّ لَهُمْ عَلَيْهَا لَشَوْبًا مِّنْ حَمِيمٍ |
68 |
Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037068.mp3
|
ثُمَّ إِنَّ مَرْجِعَهُمْ لَإِلَى الْجَحِيمِ |
69 |
Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037069.mp3
|
إِنَّهُمْ أَلْفَوْا آبَاءهُمْ ضَالِّينَ |
70 |
Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037070.mp3
|
فَهُمْ عَلَى آثَارِهِمْ يُهْرَعُونَ |
71 |
Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037071.mp3
|
وَلَقَدْ ضَلَّ قَبْلَهُمْ أَكْثَرُ الْأَوَّلِينَ |
72 |
Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037072.mp3
|
وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ |
73 |
Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037073.mp3
|
فَانظُرْ كَيْفَ كَانَ عَاقِبَةُ الْمُنذَرِينَ |
74 |
Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037074.mp3
|
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ |
75 |
Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037075.mp3
|
وَلَقَدْ نَادَانَا نُوحٌ فَلَنِعْمَ الْمُجِيبُونَ |
76 |
Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037076.mp3
|
وَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ |
77 |
Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037077.mp3
|
وَجَعَلْنَا ذُرِّيَّتَهُ هُمْ الْبَاقِينَ |
78 |
Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037078.mp3
|
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ |
79 |
Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037079.mp3
|
سَلَامٌ عَلَى نُوحٍ فِي الْعَالَمِينَ |
80 |
Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037080.mp3
|
إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ |
81 |
Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037081.mp3
|
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ |
82 |
Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037082.mp3
|
ثُمَّ أَغْرَقْنَا الْآخَرِينَ |
83 |
Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037083.mp3
|
وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِ لَإِبْرَاهِيمَ |
84 |
A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037084.mp3
|
إِذْ جَاء رَبَّهُ بِقَلْبٍ سَلِيمٍ |
85 |
A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037085.mp3
|
إِذْ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوْمِهِ مَاذَا تَعْبُدُونَ |
86 |
"Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037086.mp3
|
أَئِفْكًا آلِهَةً دُونَ اللَّهِ تُرِيدُونَ |
87 |
"To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037087.mp3
|
فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ الْعَالَمِينَ |
88 |
Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037088.mp3
|
فَنَظَرَ نَظْرَةً فِي النُّجُومِ |
89 |
Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037089.mp3
|
فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٌ |
90 |
Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037090.mp3
|
فَتَوَلَّوْا عَنْهُ مُدْبِرِينَ |
91 |
Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037091.mp3
|
فَرَاغَ إِلَى آلِهَتِهِمْ فَقَالَ أَلَا تَأْكُلُونَ |
92 |
"Me ya sãme ku, bã ku magana?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037092.mp3
|
مَا لَكُمْ لَا تَنطِقُونَ |
93 |
Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037093.mp3
|
فَرَاغَ عَلَيْهِمْ ضَرْبًا بِالْيَمِينِ |
94 |
Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037094.mp3
|
فَأَقْبَلُوا إِلَيْهِ يَزِفُّونَ |
95 |
Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/037095.mp3
|
قَالَ أَتَعْبُدُونَ مَا تَنْحِتُونَ |
96 |
"Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037096.mp3
|
وَاللَّهُ خَلَقَكُمْ وَمَا تَعْمَلُونَ |
97 |
Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037097.mp3
|
قَالُوا ابْنُوا لَهُ بُنْيَانًا فَأَلْقُوهُ فِي الْجَحِيمِ |
98 |
Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037098.mp3
|
فَأَرَادُوا بِهِ كَيْدًا فَجَعَلْنَاهُمُ الْأَسْفَلِينَ |
99 |
Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037099.mp3
|
وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَى رَبِّي سَيَهْدِينِ |
100 |
"Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037100.mp3
|
رَبِّ هَبْ لِي مِنَ الصَّالِحِينَ |
101 |
Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037101.mp3
|
فَبَشَّرْنَاهُ بِغُلَامٍ حَلِيمٍ |
102 |
To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037102.mp3
|
فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ السَّعْيَ قَالَ يَا بُنَيَّ إِنِّي أَرَى فِي الْمَنَامِ أَنِّي أَذْبَحُكَ فَانظُرْ مَاذَا تَرَى قَالَ يَا أَبَتِ افْعَلْ مَا تُؤْمَرُ سَتَجِدُنِي إِن شَاء اللَّهُ مِنَ الصَّابِرِينَ |
103 |
To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037103.mp3
|
فَلَمَّا أَسْلَمَا وَتَلَّهُ لِلْجَبِينِ |
104 |
Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm!" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037104.mp3
|
وَنَادَيْنَاهُ أَنْ يَا إِبْرَاهِيمُ |
105 |
"Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037105.mp3
|
قَدْ صَدَّقْتَ الرُّؤْيَا إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ |
106 |
Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037106.mp3
|
إِنَّ هَذَا لَهُوَ الْبَلَاء الْمُبِينُ |
107 |
Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037107.mp3
|
وَفَدَيْنَاهُ بِذِبْحٍ عَظِيمٍ |
108 |
Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037108.mp3
|
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ |
109 |
Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037109.mp3
|
سَلَامٌ عَلَى إِبْرَاهِيمَ |
110 |
Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037110.mp3
|
كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ |
111 |
Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037111.mp3
|
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ |
112 |
Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037112.mp3
|
وَبَشَّرْنَاهُ بِإِسْحَاقَ نَبِيًّا مِّنَ الصَّالِحِينَ |
113 |
Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin). |
/content/ayah/audio/hudhaify/037113.mp3
|
وَبَارَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَى إِسْحَاقَ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحْسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفْسِهِ مُبِينٌ |
114 |
Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037114.mp3
|
وَلَقَدْ مَنَنَّا عَلَى مُوسَى وَهَارُونَ |
115 |
Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037115.mp3
|
وَنَجَّيْنَاهُمَا وَقَوْمَهُمَا مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ |
116 |
Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037116.mp3
|
وَنَصَرْنَاهُمْ فَكَانُوا هُمُ الْغَالِبِينَ |
117 |
Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037117.mp3
|
وَآتَيْنَاهُمَا الْكِتَابَ الْمُسْتَبِينَ |
118 |
Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037118.mp3
|
وَهَدَيْنَاهُمَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ |
119 |
Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037119.mp3
|
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِمَا فِي الْآخِرِينَ |
120 |
Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037120.mp3
|
سَلَامٌ عَلَى مُوسَى وَهَارُونَ |
121 |
Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037121.mp3
|
إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ |
122 |
Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037122.mp3
|
إِنَّهُمَا مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ |
123 |
Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037123.mp3
|
وَإِنَّ إِلْيَاسَ لَمِنْ الْمُرْسَلِينَ |
124 |
A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037124.mp3
|
إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَلَا تَتَّقُونَ |
125 |
"Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037125.mp3
|
أَتَدْعُونَ بَعْلًا وَتَذَرُونَ أَحْسَنَ الْخَالِقِينَ |
126 |
"Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037126.mp3
|
وَاللَّهَ رَبَّكُمْ وَرَبَّ آبَائِكُمُ الْأَوَّلِينَ |
127 |
Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã). |
/content/ayah/audio/hudhaify/037127.mp3
|
فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ |
128 |
Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037128.mp3
|
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ |
129 |
Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037129.mp3
|
وَتَرَكْنَا عَلَيْهِ فِي الْآخِرِينَ |
130 |
Aminci ya tabbata ga Ilyãs. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037130.mp3
|
سَلَامٌ عَلَى إِلْ يَاسِينَ |
131 |
Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037131.mp3
|
إِنَّا كَذَلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ |
132 |
Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037132.mp3
|
إِنَّهُ مِنْ عِبَادِنَا الْمُؤْمِنِينَ |
133 |
Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037133.mp3
|
وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ الْمُرْسَلِينَ |
134 |
A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037134.mp3
|
إِذْ نَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ أَجْمَعِينَ |
135 |
Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba). |
/content/ayah/audio/hudhaify/037135.mp3
|
إِلَّا عَجُوزًا فِي الْغَابِرِينَ |
136 |
Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037136.mp3
|
ثُمَّ دَمَّرْنَا الْآخَرِينَ |
137 |
Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037137.mp3
|
وَإِنَّكُمْ لَتَمُرُّونَ عَلَيْهِم مُّصْبِحِينَ |
138 |
Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037138.mp3
|
وَبِاللَّيْلِ أَفَلَا تَعْقِلُونَ |
139 |
Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037139.mp3
|
وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ الْمُرْسَلِينَ |
140 |
A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037140.mp3
|
إِذْ أَبَقَ إِلَى الْفُلْكِ الْمَشْحُونِ |
141 |
Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037141.mp3
|
فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنْ الْمُدْحَضِينَ |
142 |
Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037142.mp3
|
فَالْتَقَمَهُ الْحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ |
143 |
To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba, |
/content/ayah/audio/hudhaify/037143.mp3
|
فَلَوْلَا أَنَّهُ كَانَ مِنْ الْمُسَبِّحِينَ |
144 |
Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037144.mp3
|
لَلَبِثَ فِي بَطْنِهِ إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ |
145 |
Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037145.mp3
|
فَنَبَذْنَاهُ بِالْعَرَاء وَهُوَ سَقِيمٌ |
146 |
Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037146.mp3
|
وَأَنبَتْنَا عَلَيْهِ شَجَرَةً مِّن يَقْطِينٍ |
147 |
Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka). |
/content/ayah/audio/hudhaify/037147.mp3
|
وَأَرْسَلْنَاهُ إِلَى مِئَةِ أَلْفٍ أَوْ يَزِيدُونَ |
148 |
Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037148.mp3
|
فَآمَنُوا فَمَتَّعْنَاهُمْ إِلَى حِينٍ |
149 |
Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza?" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037149.mp3
|
فَاسْتَفْتِهِمْ أَلِرَبِّكَ الْبَنَاتُ وَلَهُمُ الْبَنُونَ |
150 |
Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037150.mp3
|
أَمْ خَلَقْنَا الْمَلَائِكَةَ إِنَاثًا وَهُمْ شَاهِدُونَ |
151 |
To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037151.mp3
|
أَلَا إِنَّهُم مِّنْ إِفْكِهِمْ لَيَقُولُونَ |
152 |
"Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037152.mp3
|
وَلَدَ اللَّهُ وَإِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ |
153 |
Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037153.mp3
|
أَصْطَفَى الْبَنَاتِ عَلَى الْبَنِينَ |
154 |
Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037154.mp3
|
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ |
155 |
Shin, bã ku tunãni? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037155.mp3
|
أَفَلَا تَذَكَّرُونَ |
156 |
Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037156.mp3
|
أَمْ لَكُمْ سُلْطَانٌ مُّبِينٌ |
157 |
To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037157.mp3
|
فَأْتُوا بِكِتَابِكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ |
158 |
Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)" |
/content/ayah/audio/hudhaify/037158.mp3
|
وَجَعَلُوا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجِنَّةِ نَسَبًا وَلَقَدْ عَلِمَتِ الْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ |
159 |
Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037159.mp3
|
سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ |
160 |
Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037160.mp3
|
إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ |
161 |
To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/037161.mp3
|
فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ |
162 |
Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037162.mp3
|
مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَاتِنِينَ |
163 |
Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037163.mp3
|
إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ الْجَحِيمِ |
164 |
"Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037164.mp3
|
وَمَا مِنَّا إِلَّا لَهُ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ |
165 |
"Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037165.mp3
|
وَإِنَّا لَنَحْنُ الصَّافُّونَ |
166 |
"Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037166.mp3
|
وَإِنَّا لَنَحْنُ الْمُسَبِّحُونَ |
167 |
Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/037167.mp3
|
وَإِنْ كَانُوا لَيَقُولُونَ |
168 |
"Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037168.mp3
|
لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنْ الْأَوَّلِينَ |
169 |
"Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake." |
/content/ayah/audio/hudhaify/037169.mp3
|
لَكُنَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ |
170 |
Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037170.mp3
|
فَكَفَرُوا بِهِ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ |
171 |
Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037171.mp3
|
وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِينَ |
172 |
Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037172.mp3
|
إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَ |
173 |
Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037173.mp3
|
وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَ |
174 |
Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037174.mp3
|
فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّى حِينٍ |
175 |
Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037175.mp3
|
وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ |
176 |
Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/037176.mp3
|
أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ |
177 |
To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037177.mp3
|
فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَاء صَبَاحُ الْمُنذَرِينَ |
178 |
Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037178.mp3
|
وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّى حِينٍ |
179 |
Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037179.mp3
|
وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ |
180 |
Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037180.mp3
|
سُبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ |
181 |
Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037181.mp3
|
وَسَلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَ |
182 |
Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/037182.mp3
|
وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ |