Al-Hijr

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 A. L̃.R. Waɗancan ãyoyin littãfi ne da abin karantãwa mai bayyanãwa. الَرَ تِلْكَ آيَاتُ الْكِتَابِ وَقُرْآنٍ مُّبِينٍ
2 Da yawa waɗanda suka kãfirta suke gũrin dã dai sun kasance Musulmi. رُّبَمَا يَوَدُّ الَّذِينَ كَفَرُواْ لَوْ كَانُواْ مُسْلِمِينَ
3 Ka bar su su ci kuma su ji dãdi, kuma gũri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu zã su sani. ذَرْهُمْ يَأْكُلُواْ وَيَتَمَتَّعُواْ وَيُلْهِهِمُ الأَمَلُ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ
4 Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da littafi sananne. وَمَا أَهْلَكْنَا مِن قَرْيَةٍ إِلاَّ وَلَهَا كِتَابٌ مَّعْلُومٌ
5 Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba. مَّا تَسْبِقُ مِنْ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسْتَأْخِرُونَ
6 Suka ce: "Yã kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ãni) a kansa! Lalle ne kai, haƙĩƙa, mahaukaci ne." وَقَالُواْ يَا أَيُّهَا الَّذِي نُزِّلَ عَلَيْهِ الذِّكْرُ إِنَّكَ لَمَجْنُونٌ
7 "Dõmin me bã zã ka zo mana da malã'ĩku ba idan ka kasance daga mãsu gaskiya?" لَّوْ مَا تَأْتِينَا بِالْمَلائِكَةِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ
8 Bã Mu sassaukar da malã'iku fãce da gaskiya, bã zã su kasance, a wannan lõkacin, waɗanda ake yi wa jinkĩri ba. مَا نُنَزِّلُ الْمَلائِكَةَ إِلاَّ بِالحَقِّ وَمَا كَانُواْ إِذًا مُّنظَرِينَ
9 Lalle Mũ ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ãni), kuma lal1e Mũ, haƙĩƙa, Mãsu kiyayẽwane gare shi. إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ
10 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyõyin farko, gabãninka. وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا مِن قَبْلِكَ فِي شِيَعِ الأَوَّلِينَ
11 Kuma wani Manzo bã ya zuwa gare su fãce sun kasance sunã mãsu, izgili a gare shi. وَمَا يَأْتِيهِم مِّن رَّسُولٍ إِلاَّ كَانُواْ بِهِ يَسْتَهْزِئُونَ
12 Kamar wancan ne Muke shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi. كَذَلِكَ نَسْلُكُهُ فِي قُلُوبِ الْمُجْرِمِينَ
13 Bã su yin ĩmãni da shi, kuma haƙĩƙa, hanyar mutãnen farko ta shige. لاَ يُؤْمِنُونَ بِهِ وَقَدْ خَلَتْ سُنَّةُ الأَوَّلِينَ
14 Kuma dã Mun bũɗe wata ƙõfa daga sama a kansu har suka wuni a ciki sunã tãkãwa. وَلَوْ فَتَحْنَا عَلَيْهِم بَابًا مِّنَ السَّمَاء فَظَلُّواْ فِيهِ يَعْرُجُونَ
15 Lalle ne dã sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idãnuwanmu ne. Ã'a, mũ mutãne ne waɗanda aka sihirce." لَقَالُواْ إِنَّمَا سُكِّرَتْ أَبْصَارُنَا بَلْ نَحْنُ قَوْمٌ مَّسْحُورُونَ
16 Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawãta ta ga masu kallo. وَلَقَدْ جَعَلْنَا فِي السَّمَاء بُرُوجًا وَزَيَّنَّاهَا لِلنَّاظِرِينَ
17 Kuma Muka kiyãye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jĩfa. وَحَفِظْنَاهَا مِن كُلِّ شَيْطَانٍ رَّجِيمٍ
18 Fãce wanda ya sãci saurãre sai wutar yũlã bayyananniya ta bĩ shi. إِلاَّ مَنِ اسْتَرَقَ السَّمْعَ فَأَتْبَعَهُ شِهَابٌ مُّبِينٌ
19 Kuma ƙasa Mun mĩkẽ ta kuma Mun jẽfa duwãtsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunãwa da sikẽli. وَالأَرْضَ مَدَدْنَاهَا وَأَلْقَيْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ وَأَنبَتْنَا فِيهَا مِن كُلِّ شَيْءٍ مَّوْزُونٍ
20 Kuma Muka sanyã muku, a cikinta, abũbuwan rãyuwã da wanda ba ku zamã mãsu ciyarwa gare shi ba. وَجَعَلْنَا لَكُمْ فِيهَا مَعَايِشَ وَمَن لَّسْتُمْ لَهُ بِرَازِقِينَ
21 Kuma bãbu wani abu fãce a wurinMu, akwai taskõkĩnsa kuma ba Mu saukar da shi ba fãce kan gwargwado sananne. وَإِن مِّن شَيْءٍ إِلاَّ عِندَنَا خَزَائِنُهُ وَمَا نُنَزِّلُهُ إِلاَّ بِقَدَرٍ مَّعْلُومٍ
22 Kuma Muka aika iskõki mãsu barbarar jũna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shãyar da ku shi, kuma ba ku zama mãsu taskacẽwa a gare shi ba. لَوَاقِحَ فَأَنزَلْنَا مِنَ السَّمَاء مَاء فَأَسْقَيْنَاكُمُوهُ وَمَا أَنتُمْ لَهُ بِخَازِنِينَ
23 Kuma lalle ne Mu Muke rãyarwa, kuma Muke kashẽwa kuma Mũ ne magada. وَإنَّا لَنَحْنُ نُحْيِي وَنُمِيتُ وَنَحْنُ الْوَارِثُونَ
24 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun san mãsu gabãta daga cikinku, kuma Mun san mãsu jinkiri. وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَقْدِمِينَ مِنكُمْ وَلَقَدْ عَلِمْنَا الْمُسْتَأْخِرِينَ
25 Kuma lalle ne Ubangijinka Shĩ ne Yake tãra su, lalle Shĩ ne Mai hikima, Masani. وَإِنَّ رَبَّكَ هُوَ يَحْشُرُهُمْ إِنَّهُ حَكِيمٌ عَلِيمٌ
26 Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar lãka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja. وَلَقَدْ خَلَقْنَا الإِنسَانَ مِن صَلْصَالٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ
27 Kuma Aljani Mun haliccẽ shi daga gabãni, daga wutar iskar zafi. وَالْجَآنَّ خَلَقْنَاهُ مِن قَبْلُ مِن نَّارِ السَّمُومِ
28 Kuma a lõkacin da Ubangijinka ya ce wa malã'iku: "Lalle Nĩ mai halittar wani jiki ne daga ƙẽƙasasshen yumɓu wanda ya canja." وَإِذْ قَالَ رَبُّكَ لِلْمَلاَئِكَةِ إِنِّي خَالِقٌ بَشَرًا مِّن صَلْصَالٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ
29 "To idan Na daidaitã shi kuma Na hũra daga RũhĩNa a cikinsa, to, ku fãɗi a gare shi, kunã mãsu yin sujada." فَإِذَا سَوَّيْتُهُ وَنَفَخْتُ فِيهِ مِن رُّوحِي فَقَعُواْ لَهُ سَاجِدِينَ
30 Sai malã'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya. فَسَجَدَ الْمَلآئِكَةُ كُلُّهُمْ أَجْمَعُونَ
31 Fãce Iblĩs, ya ƙi kasancẽwa daga mãsu yin sujadar. إِلاَّ إِبْلِيسَ أَبَى أَن يَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ
32 Ya ce: "Yã Iblĩs mẽne ne a gare ka, ba ka kasance tãre da mãsu yin sujuda ba?" قَالَ يَا إِبْلِيسُ مَا لَكَ أَلاَّ تَكُونَ مَعَ السَّاجِدِينَ
33 Ya ce: "Ban kasance inã yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga bũsasshen yumɓun lãka wadda ta canja." قَالَ لَمْ أَكُن لِّأَسْجُدَ لِبَشَرٍ خَلَقْتَهُ مِن صَلْصَالٍ مِّنْ حَمَإٍ مَّسْنُونٍ
34 Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai abin jĩfa ne." قَالَ فَاخْرُجْ مِنْهَا فَإِنَّكَ رَجِيمٌ
35 "Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa rãnar sakamako." وَإِنَّ عَلَيْكَ اللَّعْنَةَ إِلَى يَوْمِ الدِّينِ
36 Ya ce: "Yã Ubangjĩna! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa rãnar da ake tãshin su." قَالَ رَبِّ فَأَنظِرْنِي إِلَى يَوْمِ يُبْعَثُونَ
37 Ya ce: "To, lalle ne kanã daga waɗanda ake yi wa jinkiri." قَالَ فَإِنَّكَ مِنَ الْمُنظَرِينَ
38 "Zuwa ga Yinin Lõkacin nan sananne." إِلَى يَومِ الْوَقْتِ الْمَعْلُومِ
39 Ya ce: "Yã Ubangijina! Inã rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙĩƙa inã ƙawãta musu (rãyuwa) a cikin ƙasã kuma haƙĩƙa inã ɓatar da su gabã ɗaya." قَالَ رَبِّ بِمَا أَغْوَيْتَنِي لأُزَيِّنَنَّ لَهُمْ فِي الأَرْضِ وَلأُغْوِيَنَّهُمْ أَجْمَعِينَ
40 "Fãce bãyinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake." إِلاَّ عِبَادَكَ مِنْهُمُ الْمُخْلَصِينَ
41 Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici." قَالَ هَذَا صِرَاطٌ عَلَيَّ مُسْتَقِيمٌ
42 "Lalle ne bãyĩNa, bã ka da ĩkõ a kansu, fãce wanda ya bĩ ka daga ɓatattu." إِنَّ عِبَادِي لَيْسَ لَكَ عَلَيْهِمْ سُلْطَانٌ إِلاَّ مَنِ اتَّبَعَكَ مِنَ الْغَاوِينَ
43 Kuma lalle Jahannama ce haƙĩƙa, ma'a1kawartarsu gabã ɗaya. وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمَوْعِدُهُمْ أَجْمَعِينَ
44 Tanã da ƙõfõfi bakwai, ga kõwace ƙõfa akwai wani juz'i daga gare su rababbe. لَهَا سَبْعَةُ أَبْوَابٍ لِّكُلِّ بَابٍ مِّنْهُمْ جُزْءٌ مَّقْسُومٌ
45 Lalle mãsu taƙawa sunã a cikin gidãjen Aljanna mai idandunan ruwa. إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَعُيُونٍ
46 "Ku shigẽ ta da aminci, kunã amintattu." ادْخُلُوهَا بِسَلاَمٍ آمِنِينَ
47 Kuma Muka ɗẽbe abinda ke a cikin zukãtansu na daga ƙullin zũci, suka zama 'yan'uwa a kan gadãje, sunã mãsu fuskantar junã. وَنَزَعْنَا مَا فِي صُدُورِهِم مِّنْ غِلٍّ إِخْوَانًا عَلَى سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَ
48 Wata wahala bã zã ta shãfe su bã a cikinta kuma ba su zama mãsu fita daga, cikinta ba. لاَ يَمَسُّهُمْ فِيهَا نَصَبٌ وَمَا هُم مِّنْهَا بِمُخْرَجِينَ
49 Ka bai wa bãyiNa lãbari cẽwa lalle ne Ni, Mai gãfarane, Mai jin ƙai. نَبِّئْ عِبَادِي أَنِّي أَنَا الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
50 Kuma azãbãTa ita ce azãba mai raɗaɗi. وَ أَنَّ عَذَابِي هُوَ الْعَذَابُ الأَلِيمَ
51 Kuma ka bã su lãbãrin bãƙin Ibrãhĩm. وَنَبِّئْهُمْ عَن ضَيْفِ إِ بْراَهِيمَ
52 A lõkacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mũ, daga gare ku, mãsu firgita ne." إِذْ دَخَلُواْ عَلَيْهِ فَقَالُواْ سَلامًا قَالَ إِنَّا مِنكُمْ وَجِلُونَ
53 Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mũ, munã yi makabushãra game da wani yãro masani." قَالُواْ لاَ تَوْجَلْ إِنَّا نُبَشِّرُكَ بِغُلامٍ عَلِيمٍ
54 Ya ce: "Shin kun bã ni bushãra ne a kan tsũfa yã shãfe ni? To, da me kuke bã ni bushara?" قَالَ أَبَشَّرْتُمُونِي عَلَى أَن مَّسَّنِيَ الْكِبَرُ فَبِمَ تُبَشِّرُونَ
55 Suka ce: "Munã yi maka bushãra da gaskiya ne, sabõda haka, kada da kasance daga mãsu yanke tsammãni." قَالُواْ بَشَّرْنَاكَ بِالْحَقِّ فَلاَ تَكُن مِّنَ الْقَانِطِينَ
56 Ya ce: "Kuma wãne ne yake yanke tsammãni daga rahamar Ubangijinsa, fãce ɓatattu?" قَالَ وَمَن يَقْنَطُ مِن رَّحْمَةِ رَبِّهِ إِلاَّ الضَّآلُّونَ
57 Ya ce: "To, mẽne ne babban al'amarinku? Yã kũ manzanni!" قَالَ فَمَا خَطْبُكُمْ أَيُّهَا الْمُرْسَلُونَ
58 Suka ce: "Lalle ne mũ, an aika mu zuwa ga wasu mutãne mãsu laifi." قَالُواْ إِنَّا أُرْسِلْنَا إِلَى قَوْمٍ مُّجْرِمِينَ
59 "Fãce mutãnen Lũɗu, lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu tsĩrar dasu ne gabã ɗaya." إِلاَّ آلَ لُوطٍ إِنَّا لَمُنَجُّوهُمْ أَجْمَعِينَ
60 "Fãce mãtarsa mun ƙaddara cẽwa lalle ne ita, haƙĩƙa, tanã daga mãsu halaka." إِلاَّ امْرَأَتَهُ قَدَّرْنَا إِنَّهَا لَمِنَ الْغَابِرِينَ
61 To, a lõkacin da mazannin suka jẽ wa mutãnen Lũɗu, فَلَمَّا جَاء آلَ لُوطٍ الْمُرْسَلُونَ
62 Ya ce: "Lalle ne ku mutãne ne waɗanda ba a sani ba." قَالَ إِنَّكُمْ قَوْمٌ مُّنكَرُونَ
63 Suka ce: "Ã'a, mun zo maka sabõda abin da suka kasance sunã shakka a cikinsa." قَالُواْ بَلْ جِئْنَاكَ بِمَا كَانُواْ فِيهِ يَمْتَرُونَ
64 "Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mũ, haƙĩƙa, mãsu gaskiya ne." وَأَتَيْنَاكَ بَالْحَقِّ وَإِنَّا لَصَادِقُونَ
65 "Sai ka yi tafiya da iyãlinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bãyansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku." فَأَسْرِ بِأَهْلِكَ بِقِطْعٍ مِّنَ اللَّيْلِ وَاتَّبِعْ أَدْبَارَهُمْ وَلاَ يَلْتَفِتْ مِنكُمْ أَحَدٌ وَامْضُواْ حَيْثُ تُؤْمَرُونَ
66 Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cẽwa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankẽwa ne a lõkacin da suke mãsu shiga asuba. وَقَضَيْنَا إِلَيْهِ ذَلِكَ الأَمْرَ أَنَّ دَابِرَ هَؤُلاء مَقْطُوعٌ مُّصْبِحِينَ
67 Kuma mutãnen alƙaryar suka je sunã mãsu bushãra. وَجَاء أَهْلُ الْمَدِينَةِ يَسْتَبْشِرُونَ
68 Ya ce: "Lalle ne waɗannan bãƙĩna ne, sabõda haka kada ku kunyata ni." قَالَ إِنَّ هَؤُلاء ضَيْفِي فَلاَ تَفْضَحُونِ
69 "Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki." وَاتَّقُوا اللّهَ وَلاَ تُخْزُونِ
70 Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga tãlikai ba?" قَالُوا أَوَلَمْ نَنْهَكَ عَنِ الْعَالَمِينَ
71 Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yãna idan kun kasance mãsu aikatãwa ne." قَالَ هَؤُلاء بَنَاتِي إِن كُنتُمْ فَاعِلِينَ
72 Rantsuwa da rãyuwarka! Lalle ne sũ a cikin mãyensu sunã ta ɗĩmuwa. لَعَمْرُكَ إِنَّهُمْ لَفِي سَكْرَتِهِمْ يَعْمَهُونَ
73 Sa'an nan tsãwa ta kãma su, sunã mãsu shiga lõkacin hũdõwar rãnã. فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُشْرِقِينَ
74 Sa'an nan Muka sanya samanta ya kõma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwãtsu na lãkar wuta a kansu. فَجَعَلْنَا عَالِيَهَا سَافِلَهَا وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ حِجَارَةً مِّن سِجِّيلٍ
75 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mãsu tsõkaci da hankali. إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَاتٍ لِّلْمُتَوَسِّمِينَ
76 Kuma lalle ne ita, haƙĩƙa sunã a gẽfen wata hanyã tabbatacciya. وَإِنَّهَا لَبِسَبِيلٍ مُّقيمٍ
77 Lalle ne a cikin wancan akwai ãyã ga mãsu ĩmãni. إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَةً لِّلْمُؤمِنِينَ
78 Kuma lalle ne ma'abũta Al'aika sun kasance, haƙĩƙa, mãsu zãlunci! وَإِن كَانَ أَصْحَابُ الأَيْكَةِ لَظَالِمِينَ
79 Sai Muka yi azãbar rãmuwã a gare su, kuma lalle sũ biyun, haƙĩƙa, sunã a gẽfen wani tafarki mabayyani. فَانتَقَمْنَا مِنْهُمْ وَإِنَّهُمَا لَبِإِمَامٍ مُّبِينٍ
80 Kuma lalle ne haƙĩƙa ma'abũta Hijiri sun ƙaryata Manzanni. وَلَقَدْ كَذَّبَ أَصْحَابُ الحِجْرِ الْمُرْسَلِينَ
81 Kuma Kuka kai musu ãyõyinMu, sai suka kasance mãsu bijirẽwa daga gare su. وَآتَيْنَاهُمْ آيَاتِنَا فَكَانُواْ عَنْهَا مُعْرِضِينَ
82 Kuma sun kasance sunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, alhãli sunã amintattu. وَكَانُواْ يَنْحِتُونَ مِنَ الْجِبَالِ بُيُوتًا آمِنِينَ
83 Sai tsãwa ta kãma su sunã mãsu shiga asuba. فَأَخَذَتْهُمُ الصَّيْحَةُ مُصْبِحِينَ
84 Sa'an nan abin da suka kasance sunã tsirfantãwa bai wadãtar ga barinsu ba. فَمَا أَغْنَى عَنْهُم مَّا كَانُواْ يَكْسِبُونَ
85 Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu ba fãce da gaskiya. Kuma lalle ne Sã'a (Rãnar Alƙiyãma) haƙĩƙa mai zuwa ce. Sabõdahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau. وَمَا خَلَقْنَا السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَمَا بَيْنَهُمَا إِلاَّ بِالْحَقِّ وَإِنَّ السَّاعَةَ لآتِيَةٌ فَاصْفَحِ الصَّفْحَ الْجَمِيلَ
86 Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani. إِنَّ رَبَّكَ هُوَ الْخَلاَّقُ الْعَلِيمُ
87 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bã ka bakwai waɗanda ake maimaita karatunsu da Alƙur'ãni mai girma. وَلَقَدْ آتَيْنَاكَ سَبْعًا مِّنَ الْمَثَانِي وَالْقُرْآنَ الْعَظِيمَ
88 Kada lalle kaƙĩƙa idãnunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su dãɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikãfikanka ga mãsu ĩmãni. لاَ تَمُدَّنَّ عَيْنَيْكَ إِلَى مَا مَتَّعْنَا بِهِ أَزْوَاجًا مِّنْهُمْ وَلاَ تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَاخْفِضْ جَنَاحَكَ لِلْمُؤْمِنِينَ
89 Kuma ka ce: "Lalle nĩ nĩ ne mai gargaɗi bayyananne." وَقُلْ إِنِّي أَنَا النَّذِيرُ الْمُبِينُ
90 Kamar yadda Muka saukar a kan mãsu yin rantsuwa, كَمَا أَنزَلْنَا عَلَى المُقْتَسِمِينَ
91 Waɗanda suka sanya Alƙur'ãni tãtsuniyõyi. الَّذِينَ جَعَلُوا الْقُرْآنَ عِضِينَ
92 To, rantsuwa da Ubangijinka! Haƙĩƙa, Munã tambayarsugabã ɗaya. فَوَرَبِّكَ لَنَسْأَلَنَّهُمْ أَجْمَعِيْنَ
93 Daga abin da suka kasance sunã aikatãwa. عَمَّا كَانُوا يَعْمَلُونَ
94 Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki. فَاصْدَعْ بِمَا تُؤْمَرُ وَأَعْرِضْ عَنِ الْمُشْرِكِينَ
95 Lalle ne Mũ Mun isar maka daga mãsu izgili. إِنَّا كَفَيْنَاكَ الْمُسْتَهْزِئِينَ
96 Waɗanda suke sanyãwar wani abin bautãwa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu zã su sani. الَّذِينَ يَجْعَلُونَ مَعَ اللّهِ إِلـهًا آخَرَ فَسَوْفَ يَعْمَلُونَ
97 Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã sanin cẽwa lalle kai, ƙirjinka yanã yin ƙunci game da abin da suke faɗã (na izgili). وَلَقَدْ نَعْلَمُ أَنَّكَ يَضِيقُ صَدْرُكَ بِمَا يَقُولُونَ
98 Sabõda haka ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga mãsu sujada. فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَكُن مِّنَ السَّاجِدِينَ
99 Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka. وَاعْبُدْ رَبَّكَ حَتَّى يَأْتِيَكَ الْيَقِينُ
;