1 |
Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085001.mp3
|
وَالسَّمَاء ذَاتِ الْبُرُوجِ |
2 |
Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/085002.mp3
|
وَالْيَوْمِ الْمَوْعُودِ |
3 |
Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta a cikinsa |
/content/ayah/audio/hudhaify/085003.mp3
|
وَشَاهِدٍ وَمَشْهُودٍ |
4 |
An la'ani mutãnen rãmi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085004.mp3
|
قُتِلَ أَصْحَابُ الْأُخْدُودِ |
5 |
Wato wuta wadda aka hura. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085005.mp3
|
النَّارِ ذَاتِ الْوَقُودِ |
6 |
A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085006.mp3
|
إِذْ هُمْ عَلَيْهَا قُعُودٌ |
7 |
Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085007.mp3
|
وَهُمْ عَلَى مَا يَفْعَلُونَ بِالْمُؤْمِنِينَ شُهُودٌ |
8 |
Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085008.mp3
|
وَمَا نَقَمُوا مِنْهُمْ إِلَّا أَن يُؤْمِنُوا بِاللَّهِ الْعَزِيزِ الْحَمِيدِ |
9 |
Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085009.mp3
|
الَّذِي لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاللَّهُ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ شَهِيدٌ |
10 |
Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085010.mp3
|
إِنَّ الَّذِينَ فَتَنُوا الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُؤْمِنَاتِ ثُمَّ لَمْ يَتُوبُوا فَلَهُمْ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمْ |
11 |
Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085011.mp3
|
إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ جَنَّاتٌ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ذَلِكَ الْفَوْزُ الْكَبِيرُ |
12 |
Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085012.mp3
|
إِنَّ بَطْشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ |
13 |
Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa). |
/content/ayah/audio/hudhaify/085013.mp3
|
إِنَّهُ هُوَ يُبْدِئُ وَيُعِيدُ |
14 |
Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085014.mp3
|
وَهُوَ الْغَفُورُ الْوَدُودُ |
15 |
Mai Al'arshi mai girma |
/content/ayah/audio/hudhaify/085015.mp3
|
ذُو الْعَرْشِ الْمَجِيدُ |
16 |
Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085016.mp3
|
فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ |
17 |
Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085017.mp3
|
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ الْجُنُودِ |
18 |
Fir'auna da samũdãwa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/085018.mp3
|
فِرْعَوْنَ وَثَمُودَ |
19 |
Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085019.mp3
|
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا فِي تَكْذِيبٍ |
20 |
Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da saninSa). |
/content/ayah/audio/hudhaify/085020.mp3
|
وَاللَّهُ مِن وَرَائِهِم مُّحِيطٌ |
21 |
Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085021.mp3
|
بَلْ هُوَ قُرْآنٌ مَّجِيدٌ |
22 |
A cikin Allo tsararre. |
/content/ayah/audio/hudhaify/085022.mp3
|
فِي لَوْحٍ مَّحْفُوظٍ |