1 |
Idan sama ta kẽce, |
/content/ayah/audio/hudhaify/084001.mp3
|
إِذَا السَّمَاء انشَقَّتْ |
2 |
Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron, |
/content/ayah/audio/hudhaify/084002.mp3
|
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ |
3 |
Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta, |
/content/ayah/audio/hudhaify/084003.mp3
|
وَإِذَا الْأَرْضُ مُدَّتْ |
4 |
Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084004.mp3
|
وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ |
5 |
Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren, |
/content/ayah/audio/hudhaify/084005.mp3
|
وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ |
6 |
Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084006.mp3
|
يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَى رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَاقِيهِ |
7 |
To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084007.mp3
|
فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ |
8 |
To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084008.mp3
|
فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا |
9 |
Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084009.mp3
|
وَيَنقَلِبُ إِلَى أَهْلِهِ مَسْرُورًا |
10 |
Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084010.mp3
|
وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ وَرَاء ظَهْرِهِ |
11 |
To, zã shi dinga kiran halaka! |
/content/ayah/audio/hudhaify/084011.mp3
|
فَسَوْفَ يَدْعُو ثُبُورًا |
12 |
Kuma ya shiga sa'ĩr. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084012.mp3
|
وَيَصْلَى سَعِيرًا |
13 |
Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084013.mp3
|
إِنَّهُ كَانَ فِي أَهْلِهِ مَسْرُورًا |
14 |
Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084014.mp3
|
إِنَّهُ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ |
15 |
Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084015.mp3
|
بَلَى إِنَّ رَبَّهُ كَانَ بِهِ بَصِيرًا |
16 |
To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084016.mp3
|
فَلَا أُقْسِمُ بِالشَّفَقِ |
17 |
Da dare, da abin da ya ƙunsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084017.mp3
|
وَاللَّيْلِ وَمَا وَسَقَ |
18 |
Da watã idan (haskensa) ya cika. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084018.mp3
|
وَالْقَمَرِ إِذَا اتَّسَقَ |
19 |
Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084019.mp3
|
لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ |
20 |
To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni? |
/content/ayah/audio/hudhaify/084020.mp3
|
فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ |
21 |
Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u? |
/content/ayah/audio/hudhaify/084021.mp3
|
وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لَا يَسْجُدُونَ |
22 |
Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084022.mp3
|
بَلِ الَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ |
23 |
Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084023.mp3
|
وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ |
24 |
Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084024.mp3
|
فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ |
25 |
Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/084025.mp3
|
إِلَّا الَّذِينَ آمَنُواْ وَعَمِلُواْ الصَّالِحَاتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ |