1 |
Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083001.mp3
|
وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ |
2 |
Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083002.mp3
|
الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُواْ عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ |
3 |
Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa |
/content/ayah/audio/hudhaify/083003.mp3
|
وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ |
4 |
Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/083004.mp3
|
أَلَا يَظُنُّ أُولَئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ |
5 |
Domin yini mai girma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083005.mp3
|
لِيَوْمٍ عَظِيمٍ |
6 |
Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta? |
/content/ayah/audio/hudhaify/083006.mp3
|
يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ |
7 |
Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083007.mp3
|
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ |
8 |
Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn? |
/content/ayah/audio/hudhaify/083008.mp3
|
وَمَا أَدْرَاكَ مَا سِجِّينٌ |
9 |
Wani 1ittãfi ne rubũtacce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083009.mp3
|
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ |
10 |
Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083010.mp3
|
وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ |
11 |
Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083011.mp3
|
الَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوْمِ الدِّينِ |
12 |
Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083012.mp3
|
وَمَا يُكَذِّبُ بِهِ إِلَّا كُلُّ مُعْتَدٍ أَثِيمٍ |
13 |
Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083013.mp3
|
إِذَا تُتْلَى عَلَيْهِ آيَاتُنَا قَالَ أَسَاطِيرُ الْأَوَّلِينَ |
14 |
A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083014.mp3
|
كَلَّا بَلْ رَانَ عَلَى قُلُوبِهِم مَّا كَانُوا يَكْسِبُونَ |
15 |
A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083015.mp3
|
كَلَّا إِنَّهُمْ عَن رَّبِّهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّمَحْجُوبُونَ |
16 |
Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083016.mp3
|
ثُمَّ إِنَّهُمْ لَصَالُوا الْجَحِيمِ |
17 |
Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi." |
/content/ayah/audio/hudhaify/083017.mp3
|
ثُمَّ يُقَالُ هَذَا الَّذِي كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ |
18 |
A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna? |
/content/ayah/audio/hudhaify/083018.mp3
|
كَلَّا إِنَّ كِتَابَ الْأَبْرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ |
19 |
Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna? |
/content/ayah/audio/hudhaify/083019.mp3
|
وَمَا أَدْرَاكَ مَا عِلِّيُّونَ |
20 |
Wani littãfi ne rubũtacce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083020.mp3
|
كِتَابٌ مَّرْقُومٌ |
21 |
Muƙarrabai suke halarta shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083021.mp3
|
يَشْهَدُهُ الْمُقَرَّبُونَ |
22 |
Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083022.mp3
|
إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ |
23 |
A kan karagu, suna ta kallo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083023.mp3
|
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ |
24 |
Kana sani a cikin huskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083024.mp3
|
تَعْرِفُ فِي وُجُوهِهِمْ نَضْرَةَ النَّعِيمِ |
25 |
Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083025.mp3
|
يُسْقَوْنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخْتُومٍ |
26 |
¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083026.mp3
|
خِتَامُهُ مِسْكٌ وَفِي ذَلِكَ فَلْيَتَنَافَسِ الْمُتَنَافِسُونَ |
27 |
Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083027.mp3
|
وَمِزَاجُهُ مِن تَسْنِيمٍ |
28 |
(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083028.mp3
|
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا الْمُقَرَّبُونَ |
29 |
Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083029.mp3
|
إِنَّ الَّذِينَ أَجْرَمُوا كَانُواْ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا يَضْحَكُونَ |
30 |
Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083030.mp3
|
وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمْ يَتَغَامَزُونَ |
31 |
Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083031.mp3
|
وَإِذَا انقَلَبُواْ إِلَى أَهْلِهِمُ انقَلَبُواْ فَكِهِينَ |
32 |
Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne." |
/content/ayah/audio/hudhaify/083032.mp3
|
وَإِذَا رَأَوْهُمْ قَالُوا إِنَّ هَؤُلَاء لَضَالُّونَ |
33 |
Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083033.mp3
|
وَمَا أُرْسِلُوا عَلَيْهِمْ حَافِظِينَ |
34 |
To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083034.mp3
|
فَالْيَوْمَ الَّذِينَ آمَنُواْ مِنَ الْكُفَّارِ يَضْحَكُونَ |
35 |
A kan karagu, suna ta kallo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/083035.mp3
|
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ |
36 |
Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa? |
/content/ayah/audio/hudhaify/083036.mp3
|
هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ |