Al-Infitar

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Idan sama ta tsãge. إِذَا السَّمَاء انفَطَرَتْ
2 Kuma idan taurãri suka wãtse. وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ
3 Kuma idan tẽkuna aka facce su. وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ
4 Kuma idan kaburbura aka tõne su. وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ
5 Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar. عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ
6 Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci. يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ
7 Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka. الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ
8 A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta. فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاء رَكَّبَكَ
9 A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako! كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ
10 Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara. وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ
11 Mãsu daraja, marubũta. كِرَامًا كَاتِبِينَ
12 Sunã sanin abin da kuke aikatãwa. يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ
13 Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima. إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ
14 Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm. وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ
15 Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako. يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ
16 Bã zã su faku daga gare ta ba. وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ
17 Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako? وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ
18 Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako? ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ
19 Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake. يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِلَّهِ
;