At-Takwir

Change Language
Change Surah
Change Recitation

Hausa: Abubakar Mahmoud Gumi

Play All
# Translation Ayah
1 Idan rãna aka shafe haskenta إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ
2 Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani). وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ
3 Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su. وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ
4 Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba. وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ
5 Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su. وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ
6 Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta. وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ
7 Kuma idan rãyuka aka haɗa su da jikunkunansu. وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ
8 Kuma idan wadda aka turbuɗe ta da rai aka tambaye ta. وَإِذَا الْمَوْؤُودَةُ سُئِلَتْ
9 "Sabõda wane laifi ne aka kashe ta?" بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ
10 Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su). وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ
11 Kuma idan sama aka fẽɗe ta. وَإِذَا السَّمَاء كُشِطَتْ
12 Kuma idan Jahĩm aka hũra ta وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ
13 Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita. وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ
14 Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan). عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْ
15 To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã ba. فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ
16 Mãsu gudu suna ɓũya. الْجَوَارِ الْكُنَّسِ
17 Da dare idan ya bãyar da bãya. وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ
18 Da sãfiya idan ta yi lumfashi. وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ
19 Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah. إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ
20 Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi. ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ
21 Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce. مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ
22 Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne. وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ
23 Kuma lalle ne, yã gan shi a cikin sararin sama mabayyani. وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ
24 Kuma shi, ga gaibi bã mai rowa ba ne. وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ
25 Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce. وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ
26 Shin, a inã zã ku tafi? فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ
27 Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai. إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ
28 Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu. لِمَن شَاء مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ
29 Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda. وَمَا تَشَاؤُونَ إِلَّا أَن يَشَاء اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ
;