1 |
Yã game huska kuma ya jũya bãya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080001.mp3
|
عَبَسَ وَتَوَلَّى |
2 |
Sabõda makãho yã je masa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080002.mp3
|
أَن جَاءهُ الْأَعْمَى |
3 |
To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080003.mp3
|
وَمَا يُدْرِيكَ لَعَلَّهُ يَزَّكَّى |
4 |
Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi? |
/content/ayah/audio/hudhaify/080004.mp3
|
أَوْ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ الذِّكْرَى |
5 |
Amma wanda ya wadãtu da dũkiya. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080005.mp3
|
أَمَّا مَنِ اسْتَغْنَى |
6 |
Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi! |
/content/ayah/audio/hudhaify/080006.mp3
|
فَأَنتَ لَهُ تَصَدَّى |
7 |
To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba? |
/content/ayah/audio/hudhaify/080007.mp3
|
وَمَا عَلَيْكَ أَلَّا يَزَّكَّى |
8 |
Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080008.mp3
|
وَأَمَّا مَن جَاءكَ يَسْعَى |
9 |
Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080009.mp3
|
وَهُوَ يَخْشَى |
10 |
Kai kuma kã shagala ga barinsa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/080010.mp3
|
فَأَنتَ عَنْهُ تَلَهَّى |
11 |
A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080011.mp3
|
كَلَّا إِنَّهَا تَذْكِرَةٌ |
12 |
Sabõda wanda ya so ya tunaShi (Allah). |
/content/ayah/audio/hudhaify/080012.mp3
|
فَمَن شَاء ذَكَرَهُ |
13 |
(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa, |
/content/ayah/audio/hudhaify/080013.mp3
|
فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ |
14 |
Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080014.mp3
|
مَّرْفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةٍ |
15 |
A cikin hannãyen mala'iku marubũta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080015.mp3
|
بِأَيْدِي سَفَرَةٍ |
16 |
Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080016.mp3
|
كِرَامٍ بَرَرَةٍ |
17 |
An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa! |
/content/ayah/audio/hudhaify/080017.mp3
|
قُتِلَ الْإِنسَانُ مَا أَكْفَرَهُ |
18 |
Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi? |
/content/ayah/audio/hudhaify/080018.mp3
|
مِنْ أَيِّ شَيْءٍ خَلَقَهُ |
19 |
Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye). |
/content/ayah/audio/hudhaify/080019.mp3
|
مِن نُّطْفَةٍ خَلَقَهُ فَقَدَّرَهُ |
20 |
Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080020.mp3
|
ثُمَّ السَّبِيلَ يَسَّرَهُ |
21 |
Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080021.mp3
|
ثُمَّ أَمَاتَهُ فَأَقْبَرَهُ |
22 |
Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080022.mp3
|
ثُمَّ إِذَا شَاء أَنشَرَهُ |
23 |
Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari). |
/content/ayah/audio/hudhaify/080023.mp3
|
كَلَّا لَمَّا يَقْضِ مَا أَمَرَهُ |
24 |
To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080024.mp3
|
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ إِلَى طَعَامِهِ |
25 |
Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080025.mp3
|
أَنَّا صَبَبْنَا الْمَاء صَبًّا |
26 |
Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080026.mp3
|
ثُمَّ شَقَقْنَا الْأَرْضَ شَقًّا |
27 |
Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080027.mp3
|
فَأَنبَتْنَا فِيهَا حَبًّا |
28 |
Da inabi da ciyãwa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080028.mp3
|
وَعِنَبًا وَقَضْبًا |
29 |
Da zaitũni da itãcen dabĩno. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080029.mp3
|
وَزَيْتُونًا وَنَخْلًا |
30 |
Da lambuna, mãsu yawan itãce. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080030.mp3
|
وَحَدَائِقَ غُلْبًا |
31 |
Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080031.mp3
|
وَفَاكِهَةً وَأَبًّا |
32 |
Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080032.mp3
|
مَّتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ |
33 |
To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080033.mp3
|
فَإِذَا جَاءتِ الصَّاخَّةُ |
34 |
Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080034.mp3
|
يَوْمَ يَفِرُّ الْمَرْءُ مِنْ أَخِيهِ |
35 |
Da uwarsa da ubansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080035.mp3
|
وَأُمِّهِ وَأَبِيهِ |
36 |
Da mãtarsa da ɗiyansa. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080036.mp3
|
وَصَاحِبَتِهِ وَبَنِيهِ |
37 |
Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080037.mp3
|
لِكُلِّ امْرِئٍ مِّنْهُمْ يَوْمَئِذٍ شَأْنٌ يُغْنِيهِ |
38 |
Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080038.mp3
|
وُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ مُّسْفِرَةٌ |
39 |
Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080039.mp3
|
ضَاحِكَةٌ مُّسْتَبْشِرَةٌ |
40 |
Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080040.mp3
|
وَوُجُوهٌ يَوْمَئِذٍ عَلَيْهَا غَبَرَةٌ |
41 |
Baƙi zai rufe su. |
/content/ayah/audio/hudhaify/080041.mp3
|
تَرْهَقُهَا قَتَرَةٌ |
42 |
Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu). |
/content/ayah/audio/hudhaify/080042.mp3
|
أُوْلَئِكَ هُمُ الْكَفَرَةُ الْفَجَرَةُ |